Sanatan APC Ya Kushe Gwamna, Ya Fadawa Mutanen Jiharsa ‘Dan Takaran da Za a Zaba
- Ibikunle Amosun ya fadawa magoya bayansa su zabi Jam’iyyar African Democratic Congress
- Tsohon Gwamnan jihar Ogun bai goyon bayan tazarcen Dapo Abiodun a Jam’iyyar APC a zaben 2023
- Amosun yana so Biyi Otegbeye ya zama Gwamna, ya zargi magajinsa da jawowa jihar Ogun cibaya
Ogun - Ibikunle Amosun ya fara tallata ‘dan takararsa a zaben Gwamna, yana kira ga jama’ansa da su zabi Biyi Otegbeye na jam’iyyar ADC.
Punch ta kawo rahoto cewa Sanatan Ogun ta tsakiya a majalisar dattawa, Ibikunle Amosun ya taya Biyi Otegbeye yawon kamfe a Ado-Odo/Ota.
Baya ga garin Sagamu, tsohon Gwamnan ya zagaya da ‘dan takaran jam’iyyar ADC, Otegbeye, yana tallata shi a wasu kananan hukumomin.
Darektan yada labarai na kwamitin neman takarar ADC a zaben Gwamnan Ogun, Raheem Ajayi ya rahoto Amosun yana mai yabon Otegbeye.
Amosun ya ce Otegbeye alheri
A cewar Sanatan mai-ci, Otegbeye mai neman kujerar Gwamna a jam’iyyar ADC ya dace a zaba domin ya kawowa mutanen jihar Ogun cigaba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Amosun wanda ya yi Gwamna tsakanin 2011 da 2019 ya soki Gwamnatin Dapo Abiodun, ya ce abubuwa sun sukurkuce a karkashin mulkinsa.
Jawabin Ibikunle Amosun
"Da a ce Gwamnatin nan ta damu da tazarce, da jihar Ogun ta cigaba zuwa yanzu. Amma me aka samu zuwa yau? Cibaya.
Wannan ya jawo na fito; shiyasa na ke cewa dole mu koma tafarkin cigaba, mu koma kan tafarkin da aka san jihar Ogun.
Wani ya zo ya rage titinmu mai sahu shida zuwa sahu biyu. Akwai wata hikima nan? Ka da mu dawo da hannun agogo baya."
- Ibikunle Amosun
Saboda haka aka rahoto ‘dan siyasar yana mai kira ga mutanensa su zabi jam’iyyar ADC a zaben Gwamna, kuma su tabbatar ba ayi masu magudi.
Shi kuma Otegbeye ya yi alkawarin zai kawo ayyukan yi, ya yi abin da jama’a za su yi alfahari da shi.
Zaben Gwamnonin jihohi
Kun ji labari cewa akwai Jihohin da alamu suka nuna za a gwabza a zaben Gwamna bayan ganin yadda sakamakon zaben Shugaban Kasa ya kasance.
Isa Ashiru Kudan zai iya hana APC cigaba da mulki kamar yadda tazarcen APC yake lilo a Katsina, APC ba za ta so ta NNPP ta wulakanta ta a Kano ba.
Asali: Legit.ng