Atiku Abubakar ya Samu Hujja, ya Dage Sai Shugaban Hukumar INEC Ya Ajiye Aikinsa

Atiku Abubakar ya Samu Hujja, ya Dage Sai Shugaban Hukumar INEC Ya Ajiye Aikinsa

  • Atiku Abubakar ya yi magana da jin INEC ta ce za a hukunta wadanda suka saba a zaben Shugaban kasa
  • ‘Dan takaran Shugaban kasa a PDP ya ce da jin wannan bayani ya nuna akwai sakacin Mahmood Yakubu
  • Tun da hukumar INEC ta amsa cewa an samu matsaloli, Atiku ya ce Farfesa Mahmood Yakubu ya sauka

Abuja - Atiku Abubakar wanda ya tsaya takarar shugabancin kasa a jam’iyyar PDP ya bukaci Mahmood Yakubu ya sauka daga kujerar da yake kai.

The Cable ta rahoto ‘dan takaran yana mai cewa akwai bukatar Farfesa Mahmood Yakubu ya ajiye mukaminsa na shugaban hukumar INEC a Najeriya.

Mai taimakawa ‘dan takaran wajen yada labarai, Phrank Shaibu ya fitar da jawabi inda ya zargi shugaban INEC da kokarin daura laifi ga ma’aikatansa.

A maimakon ya yarda ya yi sakaci a zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya, Mista Phrank Shaibu ya ce Farfesa Yakubu ya fake da wasu.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: INEC Ta Haramtawa Wasu Mutane Shiga Zaben Gwamnoni, Ta Dauki Mataki Mai Zafi

Atiku ya zargi Yakubu da munafunci

A cewar Hadimin ‘dan takaran jam’iyyar hamayyar, shugaban hukumar zaben munafuki ne.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

"Bayan ya yi alkawarin daura sakamakon zaben rumfunan zabe a nan-take, sai ya bari aka yi amfani da shi, ko kuma ya murde zabin ‘Yan Najeriya.
Abin zai ba ku mamaki cewa kwanaki bakwai da kammala zabe, ba a daura duka sakamakon zaben da aka yi a shafin ganin sakamako na INEC ba.
Zaben ya yi munin da bai yi kyawun da aka yi tunani ba kamar yadda kungiyoyin ketare har da Jakadar Amurka, Mary Beth Leonard suka fada.
A maimakon ya nemi afuwa, Shugaban hukumar INEC ya koma yana zargin wasu dabam.
Bayan kwamacalar da INEC tayi a ranar 25 ga watan Fubrairu, yana borin kunya da cewa za a hukunta duk jami’an zaben da suka yi kuskure."

Kara karanta wannan

Toh fa: Kotu ya kada hantar Tinubu, ya saurari bukatar Atiku da Obi 1 kan zaben 25 ga wata

- Phrank Shaibu

An rahoto ‘dan takaran yana cewa wannan shirme ne kurum domin babu inda hukumar za ta je ta nemo ma’aikatan da za su yi zaben jihohi.

Za a soma zanga-zanga

Ku na sane Atiku Abubakar wanda ya zo na biyu a zaben da aka yi na ranar 25 ga watan Fubrairun 2023 bai karbi sakamakon ba, ya kai kara a kotun zabe.

Kafin nan, a yau aka ji labarin Shugabannin PDP za su soma zanga-zanga a Abuja domin nunawa Hukumar INEC fushinsu kan sakamakon babban zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng