Gwamnoni 9 da Jiga-Jigan Jam’iyyar PDP Za Su Taso INEC a Gaba a Kan Nasarar Tinubu
- ‘Yan kwamitin yakin zabe, Shugabanni da Gwamnonin PDP za su shirya zanga-zanga yau a Abuja
- Jagororin adawar ba su gamsu da sakamakon zaben da ya ba APC nasara a kan Atiku Abubakar ba
- An aika goron gayyata ga Gwamnonin Delta, Sokoto, Akwa Ibom Bayelsa, Edo, Adamawa, da Bauchi
Abuja - Gwamnonin da ke mulki a karkashin jam’iyya PDP da shugabannin jam’iyyar za su fara zanga-zanga a dalilin rasa zaben shugabancin kasa.
A wani rahoto daga Daily Trust mun fahimci ‘yan majalisar gudanarwa da na aminatattu da ‘yan majalisar koli za su shiga zanga-zangar nan.
Jagororin jam’iyyar hamayyar ba za su gamsu da sakamakon zaben 2023 da APC tayi nasara ba.
Shugaban PDP na kasa, Dr. Iyorchia Ayu zai jagoranci zanga-zangar da za ayi zuwa hedikwatar hukumar zabe na kasa watau INEC da ke birnin Abuja.
Okowa za su fito tattaki
Iyorchia Ayu da Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa wanda shi ne abokin gamin Atiku Abubakar a zaben 2023 su ne ‘yan gaba-gaba a wajen tattakin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
The Cable ta ce a yau za a ga Dr. Ifeanyi Okowa da sauran shugabannin jam’iyyar ta PDP a cikin bakaken tufafi domin nunawa INEC rashin jin dadinsu.
Sanarwar Ibrahim Bashir
Darektan gudanarwa na kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar, Ibrahim Bashir ya fitar da sanar da ‘ya ‘yan jam’iyya cewa za su yi tattaki.
Malam Ibrahim Bashir ya ce za a fara wannan zanga-zanga ne daga gidan Legacy House da ke Maitaima da karfe 10:00 ns zuwa Hedikwatar INEC.
Sanarwar ta fadakar da wadanda aka gayyata da su hallara kafin lokacin da kwamitin ya tsaida.
Rahoton ya ce wadanda aka gayyata sun hada da; Dr Iyorchia Ayu, Dr. Ifeanyichukwu Okowa, Udom Emmanuel da Rt Hon Aminu Waziri Tambuwal.
Haka zalika ana gayyatar Gwamnonin Bayelsa, Edo, Adamawa, Bauchi, Taraba da Osun. Sannan an aika goro zuwa ga David Mark da Bukola Saraki.
Ana sa ran ganin Darektocin NCMC ‘yan kwamitin PCC, masu nakasa da sauran masu ruwa da tsaki.
Tseren shugabancin majalisa
Tun da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ci zaben shugaban kasa, rahoto ya zo cewa an shiga lissafin Shugabannin Majalisar Wakilai da Dattawa a 2023.
A halin yanzu a majalisar dattawa, APC na da kujeru 57, APGA 1; LP 6; NNPP 2; PDP 29; SDP 2 sai YPP na da 1, sannan tana da rinjaye a majalisar wakilai.
Asali: Legit.ng