Bai Kamata Obaseki Ya Damu da Batun Tunbuke Shi Daga Kujerar Gwamna Ba, Oshiomhole
- A ranar 11 ga watan Maris, 2023 za'a gudanar da zaben gwamnoni a Najeriya kuma tuni INEC ta yi nisa a shirye-shiryenta
- Yayin da wasu gwamnoni ke fafutukar tazarce a kan kujerunsu, wasu kuma tuni suka san makomarsu saboda rashin katabus a zangon mulkinsu
- Abin sha'awar, tsohon gwamnan Edo, Adama Oshiomhole, ya bukaci gwamna Godwin Obaseki ya kwantar da hankalinsa kar ya sa damuwa a ransa
Edo - Gabanin ranar Asabar 11 ga watan Maris, 2023 da za'a gudanar da zaben mambobin majlisar dokoki, tsohon gwamnan Edo, Adams Oshiomhole, ya aike da sako ga magajinsa.
Kwamaret Oshiomhole ya ce bai kamata wanda ya gaje shi, gwamna Godwin Obaseki, ya damu da batun tsige shi daga kan kujerarsa ba idan jam'iyyarsa ta yi rashin nasara.
Tsohon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa ya yi wannan furuci ne yayin hira da manema labarai a Benin City, babban birnin jihar Edo, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Legit.ng Hausa ta gano cewa Oshiomhole ya lashe kujerar Sanata mai wakiltar mazabar Edo ta arewa a majalisar Dattawa a zaben ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu, 2023.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jigon APC ya aika sako ga Obaseki
Tsohon gwamnan ya jaddada cewa idan har Obaseki ya yi aikin da mutane ke bukata a matsayin gwamnan Edo, bai kamata ya damu ba idan masu kada kuri'u sun ƙaurace wa PDP.
Ya kuma zargi gwamnatin Obaseki da rashin sakar wa bangaren masu yin doka mara su yi aikin da kundin mulki ya ɗora masu ba.
"Maƙasudin kafa majalisar dokoki shi ne su tantance duk wani yunkurin ɓangaren zartaswa a dokance, ba wai haka nan zasu kashe miliyoyi ba, ko ma na ce biliyoyi, dole sai an bi ta ɓangaren doka."
A cewarsa, 'yan takarar majalisar dokokin, "Sun ƙagara su tabbatar da cewa gwamna ya kashe arzikin jihar ta hanyar da mutanen mazabu suke muradi, tsige shi ba ya cikin manufofin su."
APC ta kara karfi a Gombe
A wani labarin kuma Ana dab da zaben gwamna, babban jigon siyasa da mambobi sama da 5000 sun sauya sheƙa zuwa APC
Muhammad Isa, jigon jam'iyyar ADC ya tattara magoya bayansa, ya ce sun hango kyaun goben Gombawa a karkashin mulkin gwamna Muhammad Inuwa.
Gwamna Inuwa ya musu maraba kana ya sake rokon mutane da su sake baiwa gwamnatinsa dama a karo na biyu.
Asali: Legit.ng