Jam’iyyar APC Ta Fadi ‘Dan Siyasa Mafi Hadari da Aka Taba Yi a Tarihin Najeriya
- Kwamitin yakin nemen takarar kujerar shugaban kasa a APC ya yi wa ‘Dan takaran LP martani
- Dele Alake ya ce Peter Obi ya yaudari matasa ne a zaben 2023, ya yi amfani da kabilanci da addini
- Mai ba kwamitin na APC PCC shawara yake cewa babu ta yadda Jam’iyyar LP za ta kafa gwamnati
Abuja - Kwamitin yakin nemen takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ta soki yadda Peter Obi ya yi amfani da bangaranci da addini a zaben 2023.
Punch ta rahoto Dele Alake yana sukar ‘dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar adawa ta LP yayin da yake maida masa martani kan zargin magudi.
Peter Obi yana zargin an yi murdiya kafin Bola Tinubu ya lashe zaben da aka yi, kwamitin yakin takarar jam’iyyar APC mai mulki ta musanya zargin.
Mista Dele Alake shi ne Babban mai taimakawa wajen yada labarai da sadarwa a kwamitin PCC.
LP ba za ta iya lashe zabe ba
Hadimin kwamitin takaran ya yi wa Obi shakiyanci, ya zarge shi da yaudarar matasa, ya ce a irin haka babu yadda ‘dan siyasar zai kai ga mulki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
The Nation rahoto Alake yana cewa ‘dan takaran na LP ya raba kan al’umma, ya yi amfani da yadda matasan kasar suke neman gwarzon ceto Najeriya.
Jawabin Dele Alake
"A game da Obi, tarihi zai tuna shi a matsayin ‘dan siyasar Najeriya mafi hadari da raba kan mutane. Ya yi kaimi a siyasa ne ta hanyar kamfe da addini da bangaranci.
Ya gabatar da kansa a matsayin gwarzo wanda zai shawo kan matsalolin da suka addabi kasarmu.
Ya yi amfani da raunin matasanmu da suke da buri, ba su son sauraron uzuri, su na masu neman gwarzo. Sai ya yi amfani da sa ransu da kuma motsin ransu.
Yaudara ce kurum, har abada Obi ba kowan-kowa ba ne illa tsohon Gwamnan da bai bar wani aiki da za a rika tunawa da shi a tarihi ba.
Mafi yawan matasanmu sun dauka Obi ne shugaban da ake so, amma da-damansu ba za su iya bari a binciki sabon gwarzon na su ba.
Fusatattun matasa, malamai masu ci da addini da masu yaudara da kabilanci ne suka jawo aka yi tunanin Obi zai ci zaben shugaban kasa.
- Mista Dele Alake
A cewar Alake, jam’iyyar LP da ba ta da isassun wakilai, ba za ta iya lashe zaben shugabancin kasa ba.
Shirin zaben Gwamnoni
Rahotonmu na dazu ya ce akwai Jihohin da alamu suka nuna za a gwabza a zaben Gwamnoni da za ayi daga ganin sakamakon zaben Shugaban Kasa.
A zaben Gwamnonin jihohi, APC ba za ta so Jam’iyyar NNPP ta sake wulakanta ta a jihar Kano ba, kuma Isa Ashiru Kudan zai iya dakile APC a Kaduna.
Asali: Legit.ng