Ku Da Kanku Kun Amince Akwai Kura-Kurai A Zaben, Atiku Ya Fada Wa Bangaren Tinubu
- Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2023 ya ce jam'iyyar APC ta amsa cewa akwai kura-kurai a zaben 2023
- Atikun ya ce ikirarin da jam'iyyar APC ta yi na cewa an tafka magudin zabe a yankin kudu maso gabas ya gasgata matsayinsa, don haka ya ke son a soke zaben
- Tun bayan da hukumar INEC ta ayyana Bola Tinubu na APC a matsayin wanda ya lashe zaben ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu, PDP da LP sunce ba su yarda ba kuma za su kotu
Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce ikirarin da kwamitin kamfen din Tinubu ta yi na cewa an tafka magudin zabe hujja ne da ke tabatar da akwai kura-kurai a zaben, Daily Trust ta rahoto.
A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Juma'a a Abuja, mataimakin Atiku na musamman kan bangaren watsa labarai, Mr Phrank Shuaibu, ya ce dan takarar shugaban kasar na PDP, ya ce abin takaici ne yadda kwamitin kamfen din Tinubu ke cigaba da zolayar yan Najeriya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shuaibu ya ce ana iya gani karara cewa yan Najeriya ba su son Tinubu kuma hujja ita ne yadda ya sha kaye hannun Peter Obi na jam'iyyar Labour a Legas.
Ya ce:
"Ikirarin da Festus Keyamo ya yi na cewa an tafka magudin zabe a kudu maso gabas kuma APC za ta kallubalanci kuri'un ya tabbatar da ikirarin mu na cewa an yi kura-kurai a zaben. Wannan karin dalili ne da ya sa muke neman a soke zaben.
"Shin ba abin dariya bane yadda Tinubu ke ikirarin yana son maimaita cigaban da ya kawo a Legas a sassan Najeriya amma mutanen Legas sun ki zabensa? Sun yi amfani da yan daba amma sun fadi zaben.
"Muna rokonsu da su shirya zuwa kotu. Yan Najeriya da duniya za su ga yadda APC ta sace nasarar mutane kuma su yi wa yan Najeriya bayanin abin da yasa ake ta casu a Columbia yayin da aka yi zugum a Najeriya tun bayan bayyana dan takararsu ya ci zabe."
Ban fita daga PDP ba, Fayose
Ayodele Fayose, tsohon gwamnan jihar Ekiti ya musanta cewa ya fita daga jam'iyyarsa ta PDP.
Fayose ya ce kawai ya dan koma gefe guda ne domin ya saki jiki ya yi wasu jawabai masu muhimmanci ga shugabanni a matsayinsa na kasa ba dan jam'iyya ba.
Asali: Legit.ng