Jihar Ogun: Jam'iyyun Adawa Sun Haɗe Don Kayar Da Gwamnan APC
- Ana saura kwanaki kaɗan a fara zaɓen gwamnoni jam'iyyun adawa sun haɗe kai domin kayar da gwamnan APC
- Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta haɗe da wasu jam'iyyu tara domin kawo ƙarshen mulkin gwamna Dapo Abiodun
- Ɗan takarar gwamnan APC na jihar yace haɗewar ta zama dole domin kawo ƙarshen mulkin gwamna Dapo Abiodun
Jihar Ogun- Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Ogun ta haɗa ƙarfi da ƙarfe da wasu jam'iyyu tara domin kayar da gwamnan jihar, Dapo Abiodun, a zaɓen gwamnan da za ayi na ranar 11 ga watan Maris.
Sauran jam'iyyun sune: Accord Party, Action Alliance (AA), Action Democratic Party (ADP), All Peoples Party (APP), Allied People’s Movement (APM), Because Of Our Tomorrow (BOOT party) da African Action Congress (AAC).
Sauran sune, Young Progressive Party (YPP) da New Nigeria People’s Party (NNPP). Rahoton Daily Trust
Ɗan takarar gwamnan PDP na jihar, Ladi Adebutu, yayin da yake yin jawabi ga mabobobin sauran jam'iyyun a birnin Abeokuta, yace hakan ya zama wajibi duba da yadda sakamakon zaɓen shugaban ƙasa dana ƴan majalisun tarayya ya kaya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Adebutu, wanda yake tare da mataimakin sa, Adekunle Akinlade, ya zargi jam'iyyar APC da yin maguɗi a zaɓen da ya gabata, inda ya sha alwashin cewa PDP ba zata bari jam'iyyar ta sake yi musu maguɗi ba a zaɓen gwamnan.
Yayi kira ga sauran mambobin jam'iyyar da su haɗa kai da PDP domin kawar da Dapo Abiodun, ɗan takarar gwamnan APC, inda yake cewa nasarar Abiodun zata kawo ƙarshen jihar Ogun.
A kalaman sa:
"Idan ba muyi da gaske ba mun yi aikin da ya dace muka bari ya sake komawa, mu ka bari ya cika burin shi na sake yin gwamna, zamu samu jiha wacce ta daina aikin komai kuma hakan na nufin ƙarshen ta kenan.
"Ba zamu samu damar yin hidima ga jihar ba."
Sanatan NNPP Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar PDP a Jihar Bauchi
A wani labarin na daban kuma, sanatan NNPP ya sauya sheƙa daga jam'iyyar zuwa jam'iyya mai mulki a jihar Bauchi.
Sanatan ya dai sha kaye ne a zaɓen da akayi na ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairun 2023.
Asali: Legit.ng