Sakamakon Zaben 2023: Atiku Ya Bayyana Matakin Karshe Da Zai Dauka Idan Bai Yi Nasara A Kotu Ba

Sakamakon Zaben 2023: Atiku Ya Bayyana Matakin Karshe Da Zai Dauka Idan Bai Yi Nasara A Kotu Ba

  • Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a zaben 2023 ya fadi matakin da zai dauka bayan fadi zabe
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa zai tafi kotu domin kallubalantar sakamakon zaben da ya ce an tafka magudi da saba dokokin zabe
  • Amma, Atikun ya ce idan bai iya kwato nasarar da ya ce ya samu ba a kotun, zai bar wa Allah mai sama komai don ya yi masa sakayya

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya sanar da niyyarsa na zuwa kotu domin kallubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na 2023, da ya kira 'cin zarafin' dimokradiyya, rahoton Tribune.

Da ya ke jawabi wurin taron manema labarai a ranar Alhamis a Abuja, Atiku ya ce ya tuntubi masu ruwa da tsaki kan yadda aka yi zaben, ya kuma cimma matsaya cewa ba a bi doka ba don haka dole a kallubalanci sakamakon.

Kara karanta wannan

A shirye muke: Peter Obi zai tafi kotu kan sakamakon zabe, APC ta yi martani mai zafi

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na zaben 2023 karkashin PDP yana jawabi. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Bayan tuntubar shugabannin jam'iyyar mu da yan Najeriya daga bangarori daban-daban, na yanke shawarar cewa akwai aibi tattare da yadda aka yi zaben shugaban kasa na ranar Asabar a kowanne bangare, don haka dole ne a kallubalance zaben.
"Masu sa ido kan zabe na gida da kasashen waje sun shaida hakan. Ina tunanin ba wannan tarihin Shugaba Buhari ya ke son bari ba. Ga Buhari, lokaci bai kure ba domin ya yi gyara saboda alherin kasa da yayan mu na gaba da barin tarihi mai kyau."

Zan bar wa Allah idan ban yi nasara ba, Atiku

Amma, ya nuna cewa zai bar wa Allah komai idan ya gaza samun nasara a kotu.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce duk da cewa zaben na 2023 ya bawa yan kasa damar yin garambawul, hukumar zabe ta dakile fatan da yan Najeriya ke yi na samun canji.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Amurka Ta Taya Tinubu Murna, Ta Ba Wa Sauran Yan Takara Shawara

Atiku ya kara da cewa abin da ya ke yi na kallubalantar sakamakon zaben ba don kashin kansa bane sai dai don karfafa dimokradiyya a Najeriya.

Lauyoyi kwararru sun shirya kare Atiku a kotu kyauta

A wani rahoton kun ji cewa Dele Momodu, dan jarida kuma daya cikin yan kwamitin takarar shugaban kasa na PDP ya ce akwai lauyoyi da suka shirya don kare Atiku Abubakar a kotu ba sai an biya su ba.

Momodu ya ce nasarar da Asiwaju Tinubu na APC ya samu a zaben ba bisa gaskiya bane kuma za ta bata sunan Najeriya a idon duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164