Jihohi 6 Sun Dumfari Babban Kotun Najeriya, Sun Huro Wuta a Soke Zaben Shugaban Kasa

Jihohi 6 Sun Dumfari Babban Kotun Najeriya, Sun Huro Wuta a Soke Zaben Shugaban Kasa

  • Kwamishinonin shari’ar wasu Jihohin Najeriya sun yi karar gwamnati a game da sakamakon zaben 2023
  • Jihohin Adamawa, Akwa-Ibom, Bayelsa, Delta, Edo da kuma Sokoto su na zargin INEC ba ta bi dokar ta ba
  • Mike Ozekhome, SAN ya fadawa kotun koli cewa Hukumar INEC tayi watsi da dokar zabe na shekarar 2022

Abuja - Wasu jihohin kasar nan sun kai karar gwamnatin tarayya har gaban kotun koli kan yadda aka shirya zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisa.

A rahoton da Punch ta fitar a safiyar Juma’a, an ji labari jihohin da suka je kotu sun hada da Adamawa, Akwa-Ibom, Bayelsa, sai kuma Delta, Edo da Sokoto.

Kwamishinonin shari’a na jihohin shida suka gabatar da kara a babban kotun kasar, su na tuhumar Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Tona Wadanda Suka Fatattaki Peter Obi Daga Jam’iyyar PDP Daf da Zabe

Legit.ng Hausa ta lura duka wadannan jihohi su na karkashin mulkin jam’iyyar hamayya ta PDP.

AGF zai kare kan shi a kotu

Masu shigar da karar su na tuhumar AGF da cewa ba a tattara sakamakon zaben da aka yi a jihohi 36 da birnin tarayya Abuja kamar yadda doka ta tanada ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Lauyoyin gwamnatocin jihohin sun yi ikirari hukumar INEC ba ta bi dokar zabe ta shekarar 2022 wajen tattara zaben shugaban kasa da majalisar tarayya ba.

Bola Tinubu
Bola Tinubu da Kashim Shettima a ICC Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Rahoton ya bayyana cewa Lauyan da ya tsayawa jihohin a kotun koli shi ne Mike Ozekhome.

A madadin masu kara, Mike Ozekhome SAN, ya fadawa kotu cewa jami’an INEC ba su aika sakamakon zaben da aka yi ta na’ura kamar yadda aka tsara ba.

Jihohin sun ce a sakamakon watsi da doka da ma’aikatan zabe suka yi a Najeriya, hakan ya jawo bore, zanga-zanga da suka a kasar nan da wajen Najeriya.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnoni: Buhari Ya Bada Hakuri Kan Canjin Kudi, Ya Bayyana ‘Yan Takaransa

Lauyan masu kara ya ce sashe na 47 (3) na dokar zabe ta 2022 ya bada dama ga gwamnatin tarayya ta hannun hukumar INEC ta gyara kure-kuren da tayi.

Bukatun masu kai kara

The Cable ta ce lauyan masu shigar da kara yana so kotu ta ce wajibi ne gwamnati (INEC) ta aika da sakamakon zabe ta hanyar amfani da na’urorin zamani.

Sannan jihohin sun bukaci a yanke hukunci cewa Shugaban INEC ya saba doka wajen sanar da sakamakon zaben 2023, sannan a yarda ba a bi dokar zabe ba.

Atiku: Ka tafi Dubai -APC

An samu labari Bola Tinubu ya maidawa Atiku Abubakar martanin shigar da karar zabe. Kwamitin neman takarar APC ta ce shure-shure ne Atiku yake yi.

Tinubu ya ce tun da Peter Obi da Rabiu Kwankwaso su ka bar PDP, jam’iyyar APC ta lashe zabe, sannan watsi da tsarin karba-karba ya jawo PDP ta sha kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng