Zaben 2023: Kwararrun Lauyoyi Sun Shirya Kare Atiku a Kotu ba Tare da An Biya Su ba
- Dele Momodu ya nuna za su kalubalanci nasarar da Hukumar INEC ta ba Bola Tinubu a zaben 2023
- A madadin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, Momodu ya ce PDP za ta shiga kotun zabe
- A cewar Momodu, akwai kwararrun Lauyoyin da a shirye suke su taimakawa Atiku Abubakar a kotu
Abuja - Daya daga cikin kakakin kwamitin takarar shugaban kasa a PDP, Dele Momodu, ya ce akwai Lauyoyin da sun shirya tsayawa Atiku Abubakar.
Da aka zanta da shi a tashar talabijin Channels a ranar Alhamis, Cif Dele Momodu ya nuna manyan Lauyoyi za su yi wa Atiku Abubakar aiki a kotu a kyauta.
Momodu yana da ra’ayin cewa nasarar da Bola Tinubu ya samu a zaben shugaban kasar da aka shirya a makon jiya, ya bata sunan kasar a kasashen waje.
Tsohon ‘dan jaridar yana ganin an murde zaben 2023 domin jam’iyyar APC ta cigaba da mulki.
SAN za su yi aiki kyauta
Da aka tambayi Dele Momodu yadda za su bi domin kare ‘dan takaran jam’iyyar PDP a kotu, sai ya ce akwai wasu Lauyoyin da sun shirya bada gudumuwarsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daily Trust ba ta ce Momodu ya fadi sunayen wasu daga cikin Lauyoyin da suka shirya shiga kotu a madadin PDP domin a ruguza nasarar Bola Tinubu ba.
A zaben 2019 a cikin Lauyoyin Atiku har da jiga-jigan jam’iyyarsa ta PDP irinsu Eyitayo Jegede SAN da Kabiru Tanimu Turaki SAN da aka yi takara da shi.
"Lauyoyi da-dama sun nuna za su je kotu kyauta, har da manyan Lauyoyin da sun kai matsayin SAN.
Mu na maganar tsarin da aka bi ne, ba daidaikun mutane ko ‘dan takara ba. Mu na batun zaben ne, idan da an yi abin da ya dace, babu wanda zai je kotu.
Halaccin zaman wanda ya yi nasara a zaben a kan kujerar mulki yana da alamar tambaya idan muka yi watsi da yadda aka bi wajen darewarsa.
Yadda aka bi wajen zaben yana bata mana suna a gaban idon Duniya, dole ayi wani abu a kai."
- Dele Momodu
Abin da ya kora Peter Obi - Atiku
Da a ce Peter Obi ya zauna a PDP, an ji labari Atiku Abubakar ya ce babu wani abin da zai hana shi zama abokin takararsa kamar yadda aka yi a 2019.
Wazirin Adamawa ya ce Gwamnonin PDP sun ce dole su fito da shugaban kasa da mataimaki, hakan ya jawo Peter Obi ya tsorata, ya sauya-sheka.
Asali: Legit.ng