Aisha Buhari Ta Taya Tinubu Murna, Ta Bayar Da Tabbacin Zai Cika Alƙawuran Sa Ga Ƴan Najeriya
- Uwargidan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ta godewa ƴan Najeriya bisa zaɓar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), a zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisu
- Aisha Buhari ta nuna ƙwarin guiwarta kan cewa zaɓaɓɓen shugaban ƙasar zai cika alƙawuran da ya yiwa ƴan Najeriya lokacin yaƙin neman zaɓen sa
- Uwargidan shugaban ƙasar ta kuma nuna tabbacin ta kan cewa shugabancin Tinubu zai haifarwa da ƙasar nan ɗa mai ido
Abuja- Uwargidan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari, ta nuna ƙwarin guiwar da ta ke da shi kan zaɓaɓɓen shugaban ƙasar nan, Bola Tinubu.
Aisha Buhari ta nuna ƙwarin guiwa kan cewa Boa Tinubu yana da cikakkiyar ƙwarewar da zai kawo haɗin kai, zaman lafiya da cigaba a ƙasar nan.
A wani saƙon taya murna da uwargidan shugaban ƙasar rattaɓa wa hannu sannan ta sanya a shafinta na Facebook, ranar Laraba, 1 ga watan Maris a Abuja, ta nuna fatan cewa Tinubu zai cika alƙawuran da ya yiwa ƴan ƙasa.
Aisha Buhari tace Tinubu zai yi aiki tuƙuru wajen ganin cewa ya ba mara ɗa kunya wajen cika alƙawuran da ya yiwa ƴan Najeriya lokacin yaƙin neman zaɓen sa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kalamanta:
”Ina da yaƙinin cewa shugabancin Tinubu/Shettima, zai kai ƙasar nan kan turbar da magabatan mu suka yi mata hasashe."
Aisha Buhari, ta kuma bayyana cewa nasarar da ɗan takarar ya samu a zaɓe ta samu a dalilin jajircewa, hangen nesa da kyakkyawar niyyar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar yake da ita.
Bola Tinubu na jam'iyyar APC ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasar Najeriya bayan ya doke abokan takarar sa na jam'iyyun adawa a Najeriya.
Firaministan Ingila Ya Taya Tinubu Murnar Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa
A wani labarin na daban kuma, Firaministan Ingila yayi magana ƙan nasarar da Tinubu ya samu a zaɓen shugaɓan ƙasar Najeriya.
Rishi Sunak ya bayar da tabbacin gwamnatin sa a shiiye take ta cigaba da aiki hannu da hannu da gwamnatin Tinubu, domin ƙara ƙarfafa dangantakar dake a tsakanin ƙasashen biyu.
Asali: Legit.ng