Tsohon Shugaban Kasa, Janar Babangida Ya Fito Ya Yi Maganar Zabe da Nasarar Tinubu

Tsohon Shugaban Kasa, Janar Babangida Ya Fito Ya Yi Maganar Zabe da Nasarar Tinubu

  • Ibrahim Badamasi Babangida ya yi magana a game da sakamakon zaben sabon shugaban kasa
  • Tsohon shugaban na Najeriya ya yabi aikin INEC, ya kuma kwarara yabo ga Bola Ahmed Tinubu
  • Janar Babangida ya yi kira ga al’umma, ya ce zababben shugaban kasar zai iya gyara Najeriya

Niger - Ibrahim Badamasi Babangida wanda ya rike Najeriya a lokacin soja, ya taya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu murna a kan lashe zaben bana.

Ganin ya zama zababben shugaban kasa, Tribune ta ce Ibrahim Badamasi Babangida ya yi jawabi, yana mai yi wa Bola Ahmed Tinubu barka.

Tsohon shugaban kasar ya fitar da jawabi ta ofishin yada labaransa da ke garin Minna a jihar Neja a ranar Laraba bayan jin sakamakon zabe.

Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya ya kuma jinjinawa hukumar INEC na kawo sauye-sauye a wajen harkar shirya zabe a kasar nan.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: El-Rufai ya taya Tinubu murnar lashe zabe, ya fadi abin da Tinubu zai yiwa kasa

'Yan Najeriya sun kyauta

Har ila yau, rahoton ya ce Ibrahim Babangida ya kuma yabi ‘Yan Najeriya da suka fita suka kada kuri’arsu, suka zabi Bola Tinubu ya jagorance su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Janar Babangida
Asiwaju Bola Tinubu a gidan Ibrahim Badamasi Babangida Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

"Abin farin ciki ne a ce wannan yana faruwa a yayin da nake raye. Ina mai iya bugun kirji, in ce Bola Tinubu ya cancanta da rike kujerar nan.
Ba na shakkar cewa Tinubu zai tabuka abin kirki a matsayin Shugaban Najeriya. Irinmu da muka yi mulki, mun san akwai aiki da za ayi.
Nayi imani cewa yana da duk abin da ake bukata domin kawowa Najeriya cigaba."

- Ibrahim Badamasi Babangida

Babbar yaya a Afrika

Sun ta rahoto IBB yana cewa Najeriya ta na duk abin ake nema wajen samun cigaba da karuwa domin a cigaba da yi mata kallon babba a Afrika.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun yi dabara: Gwamnan APC na Arewa ya taya Tinubu murna, ya yiwa 'yan kasa jawabi

Babangida yana ganin har yanzu kasar ba ta kai inda ya kamata ba, amma idan aka jajirce, za ayi nasara, ya yi kira ga al’umma su bada hadin-kai.

Har ila yau, an ji tsohon shugaban na Najeriya yana cewa zababben shugaban kasar ya kware wajen zakulo wdanda suka dace domin ba su mukami.

IBB yana so sauran ‘yan takara su dauki galabar da ‘dan takaran APC ya yi a matsayin zabin Ubangiji, yana mai cewa an shiga sabon babi.

Bola Tinubu a Daura

Rahoto ya zo ranar Laraba cewa zababben Shugaban Kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu da mutanensa sun ziyarci Muhammadu Buhari a Daura.

‘Dan takaran da ya yi galaba a zaben 2023 ya hadu da Shugaba Muhammadu Buhari a mahaifarsa a Katsina bayan samun takardar shaida daga INEC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng