Nasarar Obi a Legas da Abubuwan ban Mamaki 10 da suka Girgiza Al’umma a Zabe
- An kammala babban zaben 2023 a fadin Najeriya, a karshe Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya samu nasara
- Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya tabbatar da galabar APC a zaben da ya zo da abin mamaki
- Akwai abubuwan ban mamaki da suka faru wanda har gobe ‘Yan Najeriya suke magana a game da su
Rahoton nan ya tattaro abubuwa da suka zama na ban al’ajabi a a zaben da aka gudanar, ga su nan kamar haka:
1. APC ta rasa Legas
Legit.ng Hausa ta kawo rashin nasarar Bola Tinubu a jihar Legas a matsayin mafi ban mamaki a zaben bana, ba kasafai ‘dan takara yake rasa mahaifarsa a zabe ba.
2. Nasara a Aso Rock
Baya ga galaba da LP tayi a jihar Legas a kan jam’iyyar APC, Peter Obi ya lashe zabe a duka rumfuna tara da ake da su a cikin fadar shugaban kasa da ke Abuja.
3. Shugaban APC ya rasa Nasarawa
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ba ayi tunanin Abdullahi Adamu wanda yake ikirarin bai taba shan kayi ba zai sha kashi, a 2023 LP ta karbe Nasarawa, sannan APC ta rasa Sanata a mazabarsa.
4. Ifeanyi Okowa ya ji kunya
Punch ta na kawo shan kashin Dr Ifeanyi Okowa a cikin abubuwan ban mamaki. Ganin yana takara, ba ayi tunanin har ila yau LP za ta doke Gwamnan a Delta ba.
5. Katsina ta fada hannun Atiku
Atiku ya samu nasara a kan APC a jihar Katsina inda nan ne mahaifar Muhammadu Buhari. A zaben shugaban kasa da aka yi PDP da APC su na da 489,045 da 482,283.
6. El-Rufai bai kawo Zaria ba
Duk da yana cikin manyan magoya bayan takarar Tinubu, Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da APC sun ji kunya a Zariya, PDP ta samu kuri’u 62,260 a garin Gwamna.
7. Tinubu ya yi nasara a Ribas
Kuri’u 231,591 da APC ta samu a zaben 2023 a Ribas ya ba jama’a mamaki, hakan ya na nufin an doke Atiku Abubakar da Peter Obi da ke da magoya baya sosai.
8. Girman Ortom ya fadi
Mai girma Gwamna Samuel Ortom bai iya cin zaben Sanata a Benuwai ba. Ortom ya sha kashi a hannun tsohon hadiminsa, Titus Zam da ya yi takara a inuwar APC.
9. Aleiro ya nunawa Bagudu karfinsa
A Kebbi ta tsakiya, Muhammad Adamu Aleiro da ya tsallaka zuwa PDP daga APC zai zarce, ya doke gwamna mai-ci, Atiku Bagudu a zaben kujerar Majalisar dattawa.
10. Ayade, Ishaku, da sauransu
Yadda Enyinnaya Abaribe ya hana Okezie Ikpeazu zuwa majalisa, haka Jarigbe Agom-Jarigbe ya doke Ben Ayade a zaben Sanata, shi ma Gwamnan Enugu ya ci kasa.
Burin Gwamna Darius Ishaku na zama Sanata ba zai cika ba a dalilin nasarar APC a Kudancin Taraba. Gwamnonin Filato da Enugu sun gagara cin zaben Sanatansu.
11. NNPP ta sha gaban kowa a Kano
Yayin da ake zargin El-Rufai da rashin iya doke PDP a Zaria, jam’iyya mai-mulki ta gagara tsaida Rabiu Kwankwaso a Kano duk ba a dade da sanin NNPP ba.
Abin lura a zaben bana
Kun ji labari tsayawa takarar Peter Obi a LP ta nakasa PDP a jihohin Kudu maso gabas da Kudu maso kudu, hakan ya nuna an yi amfani da kabilanci.
A gefe guda, ‘Yan Yobe da Borno da ba su saba zaben PDP ba, sun zabi Jam’iyyar saboda Atiku Abubakar wanda ya fito daga yankin yana neman mulki.
Asali: Legit.ng