Gwamna Masari Ya Tattauna Da Buhari Kan Zaben Gwamnan Jihar Katsina
- Gwamnan na Jihar Katsina ya ce ya je don taya shugaba Buhari murnar lashe zaben shugaban kasa da jam'iyyar APC tayi
- Masari ya kuma bayyana cewa Buhari yafi kowa farin ciki ganin yadda APC ta lashe zabe saboda zai mika mulki ga dan jam'iyyar sa
- Aminu Masari ya bayyana abin da suka tattauna da shugaba Buhari wa yan jarida bayan kammala ganawar sirri da shugaban kasar mai barin gado
Jihar Katsina - Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyana gamsuwar kan dan takarar gwamna Katsina na jam'iyyar APC, Dikko Radda, zai lashe zabe, rahoton Premium Times.
Masari ya bayyana haka yayin da ya ke wata hira da yan jarida da yammacin Laraba lokacin da ya ziyarci shugaba Buhari a gidansa na Daura, a jihar Katsina, don taya shi murnar lashe zaben shugaban kasa da jam'iyyar APC tayi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana Tinubu na jam'iyyar APC a matsayin zababben shugaban kasa da safiyar Laraba.
Tinubu dai ya sha kayi a hannun PDP a jihar.
Masari ya saka labulle da Shugaba Muhammadu Buhari a Katsina
Ganawar ta sirri sun shafe akalla awa daya.
Da ya ke jawabi ga yan jarida bayan kammala ganawar, gwamnan ya ce ya gana da shugaban ne don shaida masa irin shirin da APC ta yi don zaben gwamnoni mai zuwa.
Masari ya ce:
''Shi (Buhari) ya fi kowa farin ciki ganin yadda APC ta yi zabe cikin lafiya da kwanciyar hankali, kamar yadda na fada a Katsina an yi zabe lafiya ba tare anyi asarar rai ba, ba tashin hankali kuma ya yi farin ciki da yadda rahoto daga waje daban daban a fadin kasar nan na cewa an gudanar da zabe lafiya.
''Kuma kun san a matsayinsa na mai barin gwado zai so samun magaji dan jam'iyyar sa, ba bukatar a tambaya ko yana cikin farin ciki. Kowa yasan amsar kuma ya ma fi dan takarar murna, hakan ya nuna irin kokarin da ya yi a gwamnatinsa kuma shine silar zaben APC."
Ya cigaba da cewa:
"Mun fara shirye-shirye don cigaban samun nasarori inda zamu duba nasarori inda kuma da kuskure mu gyara don tinkarar zaben gwamna da muke fatan APC ta lashe. Kun san mun cinye kujerun sanatoci 3 na Jihar Katsina, mun kuma samu yan majalisar tarayya 9 daga cikin 15, kuma za ku ga duk yankin Arewa maso yamma, mun fi samun majalisun tarayya fiye da kowacce jiha."
Asali: Legit.ng