Masari Ya Shiga Sallamar Masu Rike da Mukamai Tun da Aka Kunyata Tinubu a Katsina
- Gwamna Aminu Bello Masari ya shigo da Hon. Sani Ɗanlami cikin majalisar zartarwa a Katsina
- Hon. Sani Ɗanlami ya zama Kwamishinan wasanni da matasa a madadin Bishir Gambo Saulawa
- Sanarwar SSG ta ce shi kuma Bishir Saulawa ya koma ma’aikatar sifayo bayan cire Usman Nadada
Katsina - Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya canza wasu kwamishinonin gwamnatinsa, jim kadan bayan zaben shugaban kasa.
Legit.ng Hausa ta samu labari ana samun sauye-sauye a gwamnatin jihar Katsina, wanda ana zargin hakan bai rasa nasaba da yin nasarar PDP a zabe.
Sun ta ce daga cikin wadanda Mai girma Aminu Bello Masari ya kora akwai Tasiu Dandagoro, Yusuf Barmo, Fatima Ahmed da Aminu Waziri Malumfashi.
Dandagoro shi ne Kwamishinan ayyuka na Katsina. Fatima da Aminu Sakatarorin din-din-din ne, yayin da Barmo yake rike da hukumar kula da alhazai.
Majiyar mu ta ce ana tunanin wadannan mutane sun yi wa APC zagon kasa a zaben da ya gabata.
SSG ya fitar da sanarwa
Katsina Post ta ce Sakataren gwamnati, Alhaji Muntari Lawal ya bada sanarwar canza kwamishinoni biyu, sannan an nada wani sabon Kwamishina.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Hon. Bishir Gambo Saulawa ya bar ofishin Ma’aikatar matasa da wasanni, ya zama sabon Kwamishinan harkar filaye da sifayo ba tare da bata lokaci ba.
Shi kuma Hon. Sani Danlami ya koma kan kujerar Ma’aikatar matasa da wasanni da Saulawa ya bari.
Meya jawo aka yi zazzagar?
Dalilin sallamar Nadada daga kujerar Kwamishinan harkokin filaye shi ne taimakawa PDP a zaben shugaban kasa, zargin da ba mu ji ya musanya ba.
A wani rahoton kuma an ce ba a tsige Alhaji Usman Nadada ba, yana nan a majalisar zartarwa ta jihar, ya koma rike ma'aikatar kula da ayyuka na musamman.
Baya ga haka, Gwamnan ya kori shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jihar watau SEMA, Alhaji Babangida Nasamu zai bar wannan kujera da yake kai.
Buhari ya taya Tinubu murna
Kamar yadda labari ya zo da safiyar nan, Shugaban Najeriya ya taya Bola Tinubu murnar lashe zaben sabon shugaban kasa da aka yi a makon jiya.
Idan za a tuna ‘dan takaran PDP ya doke Asiwaju Bola Tinubu na APC a jihar shugaban kasar, duk da a karshe Atiku Abubakar bai samu mulki ba.
Asali: Legit.ng