Wasu Abubuwa 5 da Suka Taimakawa Bola Tinubu Wajen Samun Nasara a Zaben 2023
- An tabbaar da Asiwaju Bola Tinubu a matsayin wanda zai zama sabon Shugaban kasar Najeriya
- ‘Dan takaran Jam’iyyar APC ya doke Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a zaben bana
- Da kuri’u 8,805,420, Bola Tinubu ya zama wanda zai karbi mulki a hannun Muhammadu Buhari
A wannan rahoto, Legit.ng ta tattaro dalilan da suka taimakawa nasarar Asiwaju Bola Tinubu na jam’iyyar APC a zaben da aka shirya:
1. Karfin hali da sa rai
Asiwaju Bola Tinubu bai taba nuna alamun cire rai da samun mulki ba, babu inda ‘dan takaran ya karaya ko ya nuna yiwuwar ya sha kashi a zaben bana.
Wannan ya yi sanadiyyyar da ya sha gaban duk wani kalubale da ya fuskanta wajen yin nasara.
2. Babatun Abeokuta
Kafin ‘dan takaran ya kai ga nasara, sai da ya yi wasu jawabai biyu duka a garin Abeokuta, wadanda suke kamar barazana ga jam’iyya da gwamnati.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Da farko ya yi babatu kafin zaben tsaida gwani, na biyu ya soki tsarin canza kudi da wahalar mai.
3. Rabuwar kan abokan adawa
Kafin APC ta iya doke PDP daga mulki a 2015, sai da aka yi taron dangi. A takarar wannan karo ‘yan adawa sun rabu zuwa jam’iyyun PDP, LP da NNPP.
Rashin dunkulewar Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso da Peter Obi ya ba jam’iyyar APC nasara.
4. Gwamnonin Arewa
Kaso mai tsoka na nasarar Bola Tinubu ya fito ne daga jihohin Arewacin Najeriya. Duk da ya fito daga Kudu, ‘dan takaran ya yi galaba a yankin makwabta.
Kuri’un da APC ta samu a Zamfara, Jigawa, Neja, Benuwai da sauransu sun bada gudumuwa.
5. Tikitin Musulmi-Musulmi
Dauko Musulmi da Tinubu ya yi domin ya zama abokin takararsa ya taimaka wajen ba shi goyon wasu daga cikin mutanen Arewacin kasar nan a zaben na 2023.
Wasu malaman addini sun goyi bayan hakan a Arewa, a karshe ta tabbata yin hakan ya ceci APC.
Ba haka aka so ba
Yayin da Olusegun Obasanjo ya aika wasika, sai ga rahoto cewa cibiyoyin bincike na Amurka sun yi maganar kyawun zaben Shugaban kasar Najeriya.
Kungiyoyin IRI, IEOM, da NDI su na zargin an yi rikici a wasu wuraren, sannan INEC ta jefa jama’a cikin shakku wajen tattara sakamakon zabe a IRev.
Asali: Legit.ng