Zaɓen Shugaban Ƙasa: Manyan Dalilan Da Suka Sanya Atiku Abubakar Ya Faɗi Zaɓe

Zaɓen Shugaban Ƙasa: Manyan Dalilan Da Suka Sanya Atiku Abubakar Ya Faɗi Zaɓe

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), yayi rashin nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 wanda aka gudanar a faɗin Najeriya a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairun 2023.

Atiku, tsohon mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, yasha kashi ne a hannun Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyya mai mulki ta All progressives Congress (APC)

Tinubu da Atiku
Zaɓen Shugaban Ƙasa: Manyan Dalilan Da Suka Sanya Atiku Abubakar Ya Faɗi Zaɓe Hoto: Twitter/Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Mun yi duba kan wasu dalilan da ya sanya Atiku yayi rashin nasara a zaɓen.

1. Rigimar zaɓen fidda gwanin shugaban ƙasa da ɓatawa da gwamnonin G5

Ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka taimaka wajen samun rashin nasarar Atiku Abubakar a zaɓen shugaban ƙasa shine rigimar da ta biyo bayan zaɓen fidda gwanin shugaban ƙasa na PDP

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Da Zafi Zafi: Jam'iyyun PDP, LP, ADC Sun Buƙaci Shugaban INEC yayi Murabus Tare Da Sake Sabon Zaɓe

Zaɓen fidda gwanin an fafata ne tsakanin gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike da Atiku Abubakar. Zaɓar Atiku da aka yi ya sanya PDP tayi watsi da kiran da akai mata na kai takarar shugabancin ƙasa yankin Kudancin Najeriya.

2. Taurin kan Atiku Abubakar da rashin ɗaukar shawara

Wani babban dalilin da ya taimaka wajen shan kashin Atiku, shine taurin kan sa.

Gwamnonin G5 sun nemi lallai sai shugaban jam'iyyar na ƙasa, Iyorchia Ayu, yayi murabus tun da Atiku ya samu takarar shugabancin ƙasa. Dalilin su shine Atiku da Ayu sun fito ne daga Arewacin Najeriya.

Atiku da Ayu sun yi kunne uwar shegu ga gwamnonin duk da sanin cewa suna buƙatar su haɗa kawunan su yayin da suka tunkari babban zaɓe. Wannan shima ya taimaka wajen rashin nasarar Atiku.

3. Takarar Peter Obi

A shekarar 2018, Atiku, ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2019, ya bayyana tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, a matsayin abokin takarar sa.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2023: Atiku Ya Tumurmusa Tinubu a Bauchi, Ya Bashi Tazara Mai Yawa

A shekarar 2022, sai Peter Obi ya fice daga jam'iyyar PDP bayan ya fahimci cewa ba za a bashi tikitin takarar shugaban ƙasa ba na 2023.

Peter Obi wanda ya koma jam'iyyar Labour Party, ya zama shalelen matasa waɗanda suke kiran kan su da 'Obedients'

Samun 'Obedients', ya sanya Peter Obi ya lashe yankin da ya fito na Kudu maso Gabas.

Wannan yankin tun asali PDP ce ke yin nasara a cikin sa. Sai dai a wannan karon sun koma bayan Peter Obi, wanda ya samu nasara da rinjaye sosai a yankin.

4. Dalilin Tinubu

Wani dalili kuma da ya sanya Atiku yayi rashin nasara a zaɓen 2023, shine takarar Bola Tinubu na jam'iyyar APC.

Tinubu gogaggen ɗan siyasa ne wanda bai taɓa shan kaye ba a zaɓukan da yayi takara a ciki.

Wasu masu nazari sun yi hasashen cewa da Atiku da wani ɗan takarar daban ya fafata, da ƙila ya iya lashe zaɓen cikin ruwan sanyi.

Kara karanta wannan

INEC Ku Daure, Ku Cije Akan Gaskiya Karku Bari Matsin Lamba Yayi Tasiri Akan Ku - Atiku Abubakar

Wasu Abubuwa 5 da Suka Taimakawa Bola Tinubu Wajen Samun Nasara a Zaben 2023

A wani labarin na daban kuma, mun yi duba kan wasu abubuwa biyar da suka taimakawa Bola Tinubu, lashe zaɓen shugaban ƙasan Najeriya.

Bola Tinubu ya kayar da Atiku Abuɓakar na jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng