2023: Mutanen Mazabata Sun Yi Azumi, Sun Yanka Rakuma Da Shanu Saboda In Yi Nasara A Zabe, Ahmad Lawan
- Shugaban Majalisar dattawa Ahmed Lawan ya bayyana yadda al'umma suka dinga nuna masa kauna bayan rasa takarar sanata a farko
- Ahmed Lawan ya ce yan Yobe ta Arewa sun yi yanka da azumi duk dan yayi nasara a kotu ya kuma sake wakiltar su
- Ya kuma yabawa al'ummar yankin tare da bayyana cewa tsahon shekara 20 bai taba ganin irin kaunar da ya gani a wannan karon ba
Yobe - Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya ce al'ummar yankin da yake wakilta sun yanka, shanu, rakuma, da sauran dabbobi kuma sun yi masa azumi don ya sake wakiltar Arewacin Yobe a majalisar dattawa.
Lawan ya bayyana haka ranar Talata lokacin da ya ke bayyana yadda ya samu damar sake tsaya wa takara bayan rasawa tun a farko.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jaridar Punch ta ruwaito a ranar Asabar cewa Lawan ya sake lashe kujerar sanata a karo na biyar don wakiltar yankin a majalisar dattawa.
Shugaban majalisar dattawan ya ce dole a yabawa al'ummar Yobe ta Arewa bisa nasarar lashe zaben.
Lawan ya ce:
''Za ku iya tunawa lokacin da aka samu rudani akan waye zai wakilci Yobe ta Arewa, an mika lamarin gaban kotu.
''A babbar kotun tarayya da ke Damaturi, kotu ta mika takara ga wani nan take, washe gari, na fitar da sanarwa cewa na karbi hukuncin babbar kotun da ta bawa wani takara kuma bazan daukaka kara ba kuma da gaske nake babu kokonto akan abun da na ke yi.
''Na gamsu matuka da abin da na ke yi. Amma mutanen Yobe ta Arewa suka hada kai suka tsaya kai da fata don nuna goyon baya. Suka ce kujerar Yobe ta Arewa ba tawa bace ni kadai. Ta su ce gaba daya.''
Lokacin da na janye, al'umma ta da jam'iyya suka cigaba da fafutikan mayar da ni, Lawan
Lawal ya ce a lokacin da ya janye daga yunkurin neman kujerar amma al'ummar yankin da jam'iyyar sa, APC sun cigaba da masa fafutuka.
Ya kara da cewa:
''To sai suka ce sun yadda da ni kuma suna mutunta ra'ayi na akan abin da na fada, amma suna so su daukaka kara game da hukuncin.
''A matakin jiha, APC, jam'iyya ta, suka fara zartar da hukunci. Mai girma gwamnan Jihar Yobe shima ya saka baki, itama uwar jam'iyya ta kasa ta saka baki aka daukaka kara. Tabbas, sun fadi a kotun daukaka kara.''
Shugaban majalisar dattawan ya cigaba da cewa Allah ne ya dubi irin yankan da suka yi da kuma zuciyar mutanen kirki ya kuma bashi nasara.
Lawan ya ce:
''Allah yana da nufi akan mu, kamar yadda wani sanannen karin magana ya ke cewa kana taka Allah na tasa. Ya dubi zuciyar mutanen kirki da suka dinga azumi don ni wanda na sani da wanda ban sani ba.
Zaben 2023: Yan Daba Sun Tafi Gidan Wani Dan Gani Kashe Nin Tinubu, Sun Lakada Wa Mahaifiyarsa Duka, Sun Kona Motarsa
''Mutanen nan sun yi azumi, sun yanka shanu, har da rakuma, suka zubar da jini a kasa. Hatta tsofaffi maza da mata sun yi azumi don inyi nasara.
''kai hatta ni kaina sai da nayi azumi lokacin da naga matasan yankin sun fara azumi. Sun yi azumi na kwana uku zuwa hudu a jere suna addu'ar mu yi nasara a kotu. Kuma munyi.
''Sun yi azumi na kwana uku zuwa hudu a jere suna min addua. Sun hadu sun siyo shanu, rakuma da tumaki da kudin su don yin yanka su kuma zubar da jinin saboda ni.
''Cin wannan zaben shine mafi nasara da na samu''.
Lawan ya bayyana cewa bayan hukuncin kotun koli, lokacin da ya isa gida, sun yi farin ciki matuka shi da al'ummar da yake wakilta.
Ya ce:
''Wasu har kukan farin ciki sukeyi. A tsahon shekara 20, ban taba ganin irin wannan kauna da mutane suka nuna min ba."
Jihohin da Bola Tinubu ya lashe a zaben shugaban kasa na 2023
A wani rahoton kun ji cewa hukumar zabe, INEC, ta tabbatar da Asiwaju Bola Tinubu na APC a matsayin zababben shugaban kasar Najeriya.
INEC ta sanar da hakan ne bayan kamalla tattara sakamakon zabe daga jihohin Najeriya 36 da birnin tarayya, Abuja.
Asali: Legit.ng