Peter Obi Ya Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a Jihar Gwamnan APC

Peter Obi Ya Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a Jihar Gwamnan APC

  • Jam'iyyar Labour Party tayi biji-biji da jam'iyyun APC da PDP a zaɓen shugaban ƙasa a jihar Ebonyi
  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, ya lallasa su Tinubu da Atiku a jihar
  • Peter Obi ya samu ƙuri'u masu rinjaye sosai wanda ya ninnika na sauran ƴan takarar shugaban ƙasar

Jihar Ebonyi- Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya lashe zaɓen shugaban ƙasan da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), ta gudanar a jihar Ebonyi.

Peter Obi ya samu ƙuri'u 259,738 inda yayi nasara akan abokan takarar sa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, da na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, a sakamakon zaɓen wanda INEC ta fitar. Rahoton Channels Tv

Peter Obi
Peter Obi Ya Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a Jihar Gwamnan APC Hoto: Channels Tv
Asali: UGC

Tinubu ya zo na biyu a zaɓen inda ya samu ƙuri'u 42,402, yayin da Atiku ya zo na uku inda ya samu ƙuri'u 13,503. Ɗan takarar jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, ya zo na huɗu inda ya samu ƙuri'u. Rahoton PM News

Kara karanta wannan

Duniya Rawar Ƴan Mata: Lalong Ya Tunkuyi Ƙasa a Takarar da Yayi Ta Sanata

A zaɓen wanda aka gudanar ranar Asabar, an tantance mau kaɗa ƙuri'a mutum 337,887, daga cikin mutumvoters 1,563,529 dake da rajistar katin zaɓe a cewar hukumar INEC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hukumar INEC ta ƙara da cewa an kaɗa ƙuri'a 337,341 a zaɓen, inda daga ciki aka shigar da ƙuri'a 325,351 a matsayin halastattu, yayin da ake soke ƙuri'u 11,990.

Yadda sakamakon zaɓen yake:

Yawan waɗanda suka yi rajista, 1,563,529

Yawan masu kaɗa ƙuri'a da aka tantance, 337,887

APC 42,402

APGA 4,120

LP 259,738

PDP 13,503

NNPP 1,661

Yawan ƙuri'un da aka amince da su, 325,351

Yawan ƙuri'un da aka soke, 11,990

Yawan ƙuri'un da aka kaɗa, 337,341

Peter Obi Ya Lallasa PDP a Jihar Abokin Takarar Atiku Abubakar

A wani labarin na daban kuma, Peter Obi ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa a jihar abokin takarar Atiku Abubakar.

Ɗan takarar na jam'iyyar Labour Party, ya lallasa Atiku da Tinubu a jihar Delta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng