Zaben 2023: Tinubu Ya Yi Kasa-Kasa Da Atiku Da Obi a Jihar Kogi
- Hukumar zabe ta INEC ta sanar da sakamakon zaben shugaban kasa daga jihar Kogi
- Asiwaju Bola Tinubu na jam'iyyar APC ya lashe zabe a jihar Kogi da yawan kuri'u 240,751
- Tinubu ya lallasa sauran manyan abokan hamayyarsa da suka hada da Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP
Kogi - Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta ayyana dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na ranar Asabar a jihar Kogi.
Adadin kuri'un da kowani dan takara ya samu
Baturen zaben INEC, Farfesa Wahab Egbenwole, ya ayyana a ranar Talata cewa Tinubu ya samu kuri'u 240,751 wajen lallasa babban abokin adawarsa, Atiku Abubakar na PDP wanda ya samu 145,104.
Har ila yau, ya ce dan takarar Labour Party, Mista Peter Obi, ne ya zo na uku da kuri'u 56,217, Daily Trust ta rahoto.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya kara da cewar daga cikin masu zabe 484,884 da aka tantance don zabe a jihar, 476,038 ne suka kada kuri'u, kuma cewa kuri'u 456,790 ne aka samu a matsayin masu inganci yayin da aka yi watsi da 19,248.
Tinubu ya lashe kananan hukumomi 15 da suka hada da: Mopa/Muro, Kogi, Kabba Bunu, Ijumu, Igala/ Mela da Yagba West, Olamaboro, Ofu ,Yagba East, Dekina, Ankpa, Lokoja, Okene and dah da Ajaokuta.
A daya bangaren, Atiku ya lashe kananan hukumomi shida da suka hada da: Ogori Magogo, Adavi, Bassa, Ibaji, Okehi da Omala.
INEC ta ayyana zaben Zamfara ta tsakiya a matsayin ba kamalalle ba
A wani labarin, hukumar zabe ta INEC ta ayyana zaben majalisar dokokin tarayya na Zamfara ta tsakiya a matsayin ba kamalalle ba bayan soke wasu rumfunar zabe.
Hakazalika INEC ta ayyana zaben dan majalisar wakilai mai wakiltan mazabar tarayya na Gusau/Tsafe da aka yi a ranar Asabar a matsayin ba kamalalle ba.
Kamar yadda turawan zaben na majalisun dokokin tarayya a yankin suka sanar, hukumar zaben za ta sanar da sabon rana da za a sake zabe don cike guraben.
Asali: Legit.ng