Peter Obi Ya Lallasa PDP a Jihar Abokin Takarar Atiku Abubakar
- Ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na PDP kuma gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, ya gaza kawo wa Atiku jiharsa
- A sakamakon zaben da INEC ta sanar tun a matakin jihar, Peter Obi ne ke kan gaba da kuri'u mafi rinjaye
- Zaben bana ya zo abubuwan ban mamaki ta yadda manyan jiga-jigan siyasa suka gaza tabbatar da nasarar jam'iyyarsu a jihar da suka fito
Delta - Mista Peter Obi, ɗan takarar shugaban kasa a inuwar Labour Party, ya tumurmusa abokin karawarsa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, da zaɓen ranar Asabar a jihar Delta.
Daily Trust tace Baturen zaben INEC mai alhalin tattara sakamako a jihar, Farfesa Owunari Abraham Georgewill, ne ya sanar da haka a Asaba, babban birnin jihar Delta.
Sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a jihar ya nuna Peter Obi ne ya samu nasara da ƙuri'u 341,866, yayin da mai biye masa, Atiku na PDP ya samu kuri'u 161,600.
Legit.ng Hausa ta gano cewa sakamakon ya nuna Mista Obi ya baiwa Atiku tazarar kuri'u 180,266.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Delta mai ci, Ifeanyi Okowa, shi ne ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a zaben da ya gudana ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023 vanguard ta rahoto.
Yadda sakamakon zaɓen shugaban ƙasa ya kasance a jihar Delta
ADC - 160
ADP - 788
APC - 90,183
APGA - 3,746
APM - 1,028
APP - 493
BP - 1,016
LP - 341,866
NNPP - 3,122
MRM - 988
PDP - 161,600
PRP - 334
SDP - 3,071
YPP - 605
ZLP - 3,324
Adadin kuri'un da aka kaɗa - 615,342
Adadin kuri'un da suka lalace - 39,309
Zakamakon Zabe: Atiku Ya Samu Nasara a Sakkwato da Kebbi
A wani labarin kuma Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, ya samu nasarar lashe kuri'u mafi yawa a jihohin arewa guda biyu.
A sakamakon zaben shugaban kasa da ya fito daga bakin baturen zaɓe na jihar Kebbi, Atiku ne ya lashe jihar da kuri'u masu yawa, Bola Tinuɓu na take masa baya.
Haka zalika a jihar Sakkwato, tsohon mataimakin shugaban kasan ya sha da kyar a hannun takwaransa na jam'iyyar APC.
Asali: Legit.ng