Zuwa Yanzu APC Ta Samu Sanatoci 38, PDP Ta Lashe 21, NNPP Ta Ci Kujeru a Majalisa

Zuwa Yanzu APC Ta Samu Sanatoci 38, PDP Ta Lashe 21, NNPP Ta Ci Kujeru a Majalisa

  • A zaben da aka sanar a halin yanzu, Jam’iyyar APC ce a kan gaba da kujeru kusan 40 a Majalisa
  • Idan aka tafi a haka, APC na kan hanyar samun rinjaye a kan jam’iyyar PDP majalisar dattawa
  • Sauran jam’iyyun da suka yi nasara a zaben Sanatoci na 2023 sun kunshi LP, NNPP da YPP

Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ce ta ke da rinjaye zuwa yanzu a zabukan majalisar dattawa kamar yadda sakamakon hukumar INEC suka tabbatar.

Daily Trust ta kawo rahoto cewa jam’iyyar APC ta lashe zaben majalisar dattawa 38, yayin da PDP mai hamayya ta yi nasara a kujeru 21 da aka sanar.

Jam’iyyar LP da tayi farin jini a zaben 2023 ta samu kujerun Sanatoci hudu, sai jam’iyyar SDP tayi galaba da kujeru biyu a zaben majalisar dattawa.

Kara karanta wannan

Assha: Tsohon ministan Buhari, Dalung ya sha kaye a mazabarsa

Haka zalika jam’iyyun YPP da NNPP za su samu kujera a majalsar tarayya ta goma da za a rantsar.

Wa zai samu rinjaye a Majalisa?

Rahoton ya ce wadannan su ne kason kujeru 67 da aka sanar a zaben 2023. Sai dai babu tabbacin cewa jam’iyyar APC mai-ci za ta cigaba da rike rinjayenta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kafin a ce jam’iyya ta samu rinjaye a majalisa, sai ta na da akalla biyu bisa ukun kujeru 109. Kowace jiha ta na da Sanatoci uku, sai Abuja ta na da guda.

Shugaban majalisar dattawa
Majalisar dattawa Hoto: @TopeBrown
Asali: Facebook

A cikin sakamakon da aka samu, Sanatoci 18 sun lashe zaben tazarce ne, ragowar sun je ne a karon farko ko kuma sun taba zama ‘yan majalisar wakilai.

Shugaban majalisar dattawa na kasa, Sanata Ahmad Lawan yana cikin wadanda za su koma, amma ba tabbas ba ne shi ne zai cigaba da rike kujerar a yanzu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar Peter Obi ta ci kujerar majalisar tarayya a wata jihar PDP

Masu nazarin siyasa sun ce Godswill Akpabio na Arewa maso yammacin Akwa Ibom da Sanatan Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu su na harin shugabanci.

Sharadin zama shugaba a majalisar dattawa shi ne mutum ya zama ba sabon-shiga ba, ko dai akalla ya taba zuwa majalisar wakilai kafin zamansa Sanata.

Akwai Sanatocin da ba za su koma ba, wadanda suka fi daukar hankali su ne; Kawu Sumaila, Bala Ibn Na’Allah, Sam Egwu, Saidu Alkali da Tanko Al-Makura.

Sai Atiku ya hakura - Fayose

Ganin har shugaban jam’iyyar PDP ya rasa mazabarsa da karamar hukumarsa a Benuwai, an ji labari Ayo Fayose ya ce babu dalilin da PDP za ta koka.

Tsohon gwamnan ya bada shawara cewa Atiku Abubakar ya karbi sakamakon cikin girma, ya lallaba ya tafi Dubai, yake cewa lokaci ya yi da zai yi ritaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng