El-Rufai Ya Gagara Kawowa Tinubu Jihar Kaduna, Atiku da PDP Sun Ragargaji APC
- A Kaduna, Atiku Abubakar ya ba Bola Tinubu ratar fiye da kuri’u 150, 000 a Zaben Shugabancin Najeriya
- ‘Dan takaran APC, Bola Tinubu ya yi nasara ne a Birnin Gwari da Sanga kurum a duk fadin jihar Kaduna
- Peter Obi ya samu kuri’u kusan 300, 000 kuma ya yi galaba a kananan hukumomi bakwai a Kudancin Jihar
Kaduna - Atiku Abubakar da ya yi takara a karkashin jam’iyyar PDP ne ya yi galaba a jihar Kaduna a zaben shugaban kasa da aka gudanar a makon jiya.
Punch ta ce Alhaji Atiku Abubakar da jam’iyyarsa ta PDP sun samu kuri’u 554,360, shi kuma ‘dan takaran APC, Bola Tinubu yana biye da kuri’u 399,293.
Peter Obi ne ya zo na uku a neman kujerar shugabancin Najeriyan da kuri’u 294, 294 a jam’iyyar LP.
Duk da LP ta zo na uku ne a zaben, ‘dan takaranta ya iya yin nasara a kananan hukumomin Chikun, Kaura, Kajuru, Jaba, Kachia, Jema’a da Zango-Kataf.
Jam’iyyar hamayya ta NNPP da ta tsaida Rabiu Musa Kwankwaso ta zo na hudu da kuri’u kusan 100, 000, amma ba ta iya kawo wata karamar hukuma ba.
Birnin-Gwari ta tuna da Tinubu
Shi Bola Tinubu ya yi galaba a ne a yankin Birnin-Gwari inda aka ba shi sarautar Dakare kafin zabe, sannan ya samu nasara a karamar hukumar Sanga.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mai girma mataimakiyar Gwamnan Kaduna, Dr. Hadiza Balarabe ta fito ne daga garin Sanga.
PDP ta samu nasara da kyau
Shi kuma Wazirin Adamawa ya samu nasara a kananan hukumomi 14 da ke jihar; Giwa, Kauru, Lere, Ikara, Kagarko, Zaria, Sabon-Gari, da Makarfi.
Har ila yau, PDP ce ka kan gaba a Kaduna ta Kudu, Kaduna ta Arewa, Kudan, Igabi, Kubau da Soba
PDP ta samu kujerun Majalisa
This Day ta kawo rahoto PDP ta lashe kujerun majalisar tarayya a mazabun Jama’a/Sanga, Kauru da Zango Kataf/Jaba a zaben da aka shirya.
Dan Amos na jam’iyyar PDP ya doke Anto Usman wanda ya tsaya takara a APC. PDP ta samu kuri’u 32, 578 a zaben yayin da APC ta kare da 26,793.
A mazabar Bashir Yusuf ya yi galaba a PDP a kan Mukhtar Zakari da Isaac Auta na APC da LP. Amos Gwamna ya rike kujerar Zango Kataf/Jaba a PDP.
Asali: Legit.ng