Tinubu Yana Kan Gaba a Jihar Nasarawa, Ya Lashe Ƙananan Hukumomi 6

Tinubu Yana Kan Gaba a Jihar Nasarawa, Ya Lashe Ƙananan Hukumomi 6

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya kama hanyar lashe jihar Nasarawa
  • Bola Tinubu yana kan gaba inda ya lashe ƙananan hukumomi 6daga cikin 13 da ake da su a jihar
  • Idan ɗan takarar ya samu nasarar lashe jihar ba ƙaramin tagomashi hakan zai sanya ya samu ba

Nasarawa- Ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, yana kan gaba a jihar Nasarawa.

Asiwaju Bola Tinubu yaba abokan takarar sa rata sosai a sakamakon da hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana. Rahoton The Nation

Tinubu
Tinubu Yana Kan Gaba a Jihar Nasarawa, Ya Lashe Ƙananan Hukumomi 6 Hoto: The Nation
Asali: UGC

Ɗan takarar na jam'iyyar APC, yana kan gaba a cikin ƙananan hukumomi shida da hukumar INEC ta bayyana sakamakon zaɓen su.

Jihar Nasarawa nan ne jihar shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Adamu.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Atiku Abubakar Ya Yi Nasara, Ya Lallasa Bola Tinubu a Jihar da APC Ke Mulki

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jihar tana da ƙananan hukumomi 13, wanda ya zuwa yanzu hukumar INEC ta bayyana sakamakon 6 daga cikin su.

Asiwaju Bola Tinubu yayi nasara a ƙananan hukumomin Keana, Wamba, Obi, Keffi, Awe da Nasarawa.

Ga yadda sakamakon yake:

A ƙaramar hukumar Keana, APC ta samu ƙuri'u 7208, PDP ta samu ƙuri'u 4335, LP ta samu ƙuri'u 4002 yayin da jam'iyyar NNPP ta samu ƙuri'u 236.

A ƙaramar hukumar Wamba, jam'iyyar APC ta samu ƙuri'u 8,990, PDP ta samu ƙuri'u 4219, LP ta samu ƙuri'u 5177, sannan NNPP ta samu ƙuri'u 313.

A ƙaramar hukumar Obi, APC 10,838, PDP ta samu ƙuri'u 12,947, LP ta samu ƙuri'u 16,188, sannan jam'iyyar NNPP ta samu ƙuri'u 150.

A ƙaramar hukumar Keffi, APC ta samu ƙuri'u 13,564, PDP ta samu ƙuri'u 13,007, LP ta samu ƙuri'u 9067, sannan jam'iyyar NNPP ta samu ƙuri'u 1798.

Kara karanta wannan

Kawu Sumaila Ya Samu Nasara, Ya Yiwa Kabiru Gaya Ritaya

A ƙaramar hukumar AWE, APC 14269, PDP ta samu ƙuri'u 10416, LP ta samu ƙuri'u 4309, sannan jam'iyyar NNPP ta su ƙuri'u 570.

A ƙaramar hukumar Nasarawa, APC ta samu ƙuri'u 17241, PDP ta samu ƙuri'u 10576, LP ta samu ƙuri'u 8680, sannan jam'iyyar NNPP ta samu ƙuri'u 1380.

Daga cikin sakamakon zaɓen da aka sanar, Asiwaju Bola Tinubu, yana kan gaba a jihar, inda ɗan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ke take masa baya a jihar.

Ana cigaba da faɗin sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisun tarayya a Najeriya. Rahoton Channels Tv

A wani labarin ma daban kuma ƴan sanda sun cafke wani lakcara ɗauke da.na'irorin tantance masu kaɗa ƙuri'a.

An dai cafke lakcaran ne a wata jiha a Kudancin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng