Atiku Abubakar Ya Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a Jihar Katsina
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, yayi nasara a jihar Katsina
- Jihar Katsina a Arewacin Najeriya itace jihar da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC ya fito
- Atiku Abubakar ya lallasa Bola Tinubu na jam'iyyar APC duk kuwa da cewa Tinubu ne ya cinye mafiya yawan ƙananan hukumomin jihar
Katsina- Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya lallasa babban abokin hamayyar sa Bola Tinubu, na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Katsina.
Muazu Abubakar, jami'in tattara sakamakon zaɓen jihar, shine ya sanar da sakamakon a birnin Katsina. Rahoton Premium Times
Abubakar yace Atiku ya samu jimillar ƙuri'u 489,045 fiye da Tinubu wanda ya samu ƙuri'u 482, 283, inda aka samu tazarar 6,762. Rabiu Kwankwaso na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya samu ƙuri'u 69,386.
Duk da cewa Tinubu yayi nasara a ƙananan hukumomi 21 a jihar, Atiku wanda yayi nasara a ƙananan hukumomi 13, shine ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a jihar. Jihar Katsina tana da ƙananan hukumomi 34.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Atiku Abubakar yayi nasara a ƙananan hukumomin Batsari, Mashi, Kurfi, Batagarawa, Dutsinma, Kusada, Mani, Kankia, Kankara, Bakori, Jibia, Katsina da Safana, sannan ya samu ƙuri'u masu yawa a sauran ƙananan hukumomin. Rahoton Channels Tv
Sauran jam'iyyun sun samu ƙuri'u kamar haka, APGA - 1,391, NNPP – 69,386, Labour Party – 6,376, PRP – 1,986, SDP – 339, YPP – 1,029 da ZLP – 371
Jihar Katsina tana da yawan masu kaɗa ƙuri'a 3,516,719 amma mutum 1,097,663 kawai aka tantance domin kaɗa ƙuri'a.
A cewar jami'in tattara sakamakon zaɓen INEC, an soke zaɓe a wasu rumfunan zaɓe a ƙananan hukumomin Baure, Danmusa, Dutsinma, Funtua, Kafur, Kankara, Katsina, Kurfi, Kusada, Mai’adua, Malumfashi, Mashi, Sabuwa da Safana
Hakan ya faru ne saboda matsalar tsaro, tayar da rigima da kuma kaɗa ƙuri'a fiye da ƙa'ida.
A wani labarin na daban kuma, jam'iyyar NNPP ta kayar da ɗan gwamnan jihar Kano, a takarar majalisar tarayya.
An dai gudanar da zaɓen ne a ranar Asabar.
Asali: Legit.ng