Zabe: Kwankwaso Na Gaba Da Tinubu Atiku Da Kuri’u Masu Yawa a Kano

Zabe: Kwankwaso Na Gaba Da Tinubu Atiku Da Kuri’u Masu Yawa a Kano

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso ya nuna tasirinsa a siyasar Kano
  • Kwankwaso ya lashe kananan hukumomi tara cikin 10 da hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar zuwa yanzu
  • Ya yi wa Bola Tinubu na APC, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour Party fintinkau a kananan hukumomin na Kano

Kano - Sanata Rabiu Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) yana nuna cewa lallai shine babban dan takarar zaben 2023 a jihar Kano.

A zahirin gaskiya, yana nuna tasirinsa a siyasar Kano, domin dai Kwankwaso ne kan gaba da tazarar kuri'u masu yawa a kananan hukumomi 16 na jihar da hukumar zabe ta ayyana zuwa yanzu.

Yan takarar shugaban kasa rike da sifiku
Zabe: Kwankwaso Na Gaba Da Tinubu Atiku Da Kuri’u Masu Yawa a Kano Hoto: @atiku, @officialABAT, @KwankwasoRM, @PeterObi
Asali: Twitter

Kwankwaso ne kan gaba a jihar Kano

Kamar yadda aka sanar a cibiyar tattara sakamako na hukumar zabe a jihar, Asiwaju Bola Tinubu dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya lashe kananan hukumomi biyu, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Samu Nasara a Kananan Hukumomi 12 Na Jihar Oyo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da Peter Obi na Labour Party basu kawo karamar hukuma ko daya ba.

Ga sakamakon wasu daga cikin kananan hukumomin:

1. Karamar Hukumar Kura

APC: 10,929

LP: 126

NNPP 20,407

PDP: 3,987

2. Karamar hukumar Minjibir

A 06

APC 6777

LP 123

NNPP 15505

PDP 1833

3. Karamar Hukumar Warawa

APC 10352

LP 125

NNPP 12708

PDP 1277

4. Karamar Hukumar Gabasawa

APC 11992

LP 48

NNPP 13736

PDP -

5. Karamar Hukumar Kibiya

APC: 10,283

LP: 70

NNPP: 16,331

PDP: 753

6. Karamar hukumar Rimin Gado

APC: 10,861

LP: 76

NNPP: 14,634

PDP: 907

7. Karamar Hukumar Garun Malam

APC: 8,642

LP: 160

NNPP: 12,249

PDP: 4,409

8. Karamar Hukumar Makoda

APC: 12,590

LP: 40

NNPP: 12,247

PDP: 1,099

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar Ya Lallasa Tinubu, Ya Lashe Zabe a Kananan Hukumomi 18 Cikin 23 a Jihar Osun

9. Karamar Hukumar Sumaila

APC 11341

LP 1106

NNPP 24,3067

PDP 1553

10.Karamar Hukumar Dawakin Tofa

APC 16,773

LP 2020

NNPP 25072

PDP 2477

11. Karamar hukumar Dawakin Kudu

APC – 12,258

LP – 167

NNPP – 32,925

PDP – 3,768

12. Karamar hukumar Tofa

APC – 10,280

LP – 177

NNPP – 17,219

PDP – 1,192

13. Karamar hukumar Danbata

APC: 13179

PDP: 2099

NNPP: 15179

LP: 66

14. Karamar hukumar Rogo

NNPP - 19,587

APC - 10,043

PDP - 1,616

LP - 343

Bola Tinubu ne gaba a kananan hukumomi 12 na jihar Oyo

A wani labarin kuma, mun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu ne ke kan gaba a kananan hukumomi 12 na jihar Oyo inda ya yi wa sauran abokan hamayyarsa fintinkau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel