Zabe: Kwankwaso Na Gaba Da Tinubu Atiku Da Kuri’u Masu Yawa a Kano
- Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso ya nuna tasirinsa a siyasar Kano
- Kwankwaso ya lashe kananan hukumomi tara cikin 10 da hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar zuwa yanzu
- Ya yi wa Bola Tinubu na APC, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour Party fintinkau a kananan hukumomin na Kano
Kano - Sanata Rabiu Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) yana nuna cewa lallai shine babban dan takarar zaben 2023 a jihar Kano.
A zahirin gaskiya, yana nuna tasirinsa a siyasar Kano, domin dai Kwankwaso ne kan gaba da tazarar kuri'u masu yawa a kananan hukumomi 16 na jihar da hukumar zabe ta ayyana zuwa yanzu.
Kwankwaso ne kan gaba a jihar Kano
Kamar yadda aka sanar a cibiyar tattara sakamako na hukumar zabe a jihar, Asiwaju Bola Tinubu dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya lashe kananan hukumomi biyu, Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da Peter Obi na Labour Party basu kawo karamar hukuma ko daya ba.
Ga sakamakon wasu daga cikin kananan hukumomin:
1. Karamar Hukumar Kura
APC: 10,929
LP: 126
NNPP 20,407
PDP: 3,987
2. Karamar hukumar Minjibir
A 06
APC 6777
LP 123
NNPP 15505
PDP 1833
3. Karamar Hukumar Warawa
APC 10352
LP 125
NNPP 12708
PDP 1277
4. Karamar Hukumar Gabasawa
APC 11992
LP 48
NNPP 13736
PDP -
5. Karamar Hukumar Kibiya
APC: 10,283
LP: 70
NNPP: 16,331
PDP: 753
6. Karamar hukumar Rimin Gado
APC: 10,861
LP: 76
NNPP: 14,634
PDP: 907
7. Karamar Hukumar Garun Malam
APC: 8,642
LP: 160
NNPP: 12,249
PDP: 4,409
8. Karamar Hukumar Makoda
APC: 12,590
LP: 40
NNPP: 12,247
PDP: 1,099
9. Karamar Hukumar Sumaila
APC 11341
LP 1106
NNPP 24,3067
PDP 1553
10.Karamar Hukumar Dawakin Tofa
APC 16,773
LP 2020
NNPP 25072
PDP 2477
11. Karamar hukumar Dawakin Kudu
APC – 12,258
LP – 167
NNPP – 32,925
PDP – 3,768
12. Karamar hukumar Tofa
APC – 10,280
LP – 177
NNPP – 17,219
PDP – 1,192
13. Karamar hukumar Danbata
APC: 13179
PDP: 2099
NNPP: 15179
LP: 66
14. Karamar hukumar Rogo
NNPP - 19,587
APC - 10,043
PDP - 1,616
LP - 343
Bola Tinubu ne gaba a kananan hukumomi 12 na jihar Oyo
A wani labarin kuma, mun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu ne ke kan gaba a kananan hukumomi 12 na jihar Oyo inda ya yi wa sauran abokan hamayyarsa fintinkau.
Asali: Legit.ng