Tinubu Ya Lallasa Atiku Da Obi a Kananan Hukumomi 12 Na Jihar Oyo
- Sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu na ci gaba da fitowa daga matakin karamar hukuma
- Bola Tinubu ya yi wa Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour Party fintinkau a kananan hukumomi 12 na jihar Oyo da aka sanar zuwa yanzu
- Har yanzu ana ci gaba da tattara sakamako daga bangarori daban-daban na kasar Najeriya
Oyo - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, Bola Tinubu, ya yi kasa-kasa da yan takarar jam'iyyun Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar, and Peter Obi of the Labour Party a jihar Oyo.
Tinubu na gaba da takwarorinsu a kananan hukumomi 12 na jihar Oyo da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta sanar zuwa yanzu kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.
Ga cikakken sakamakon kananan hukumomin a kasa:
Karamar hukumar Ibadan ta arewa maso yamma
APC 13078
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
PDP 6011
LP 4820
Karamar hukumar Kajola
APC 11917
PDP 9358
LP 503
Karamar hukumar Afijio
APC 8876
PDP 4112
LP 1925
Karamar hukumar Itesiwaju
APC 6180
PDP 4948
LP 387
Karamar hukumar Atisbo
APC 7928
PDP 4031
LP 1178
Karamar hukumar Atiba
APC 15046
PDP 6180
LP 1234
Karamar hukumar Lagelu
APC 16011
PDP 5112
LP 4066
Karamar hukumar Oyo ta yamma
APC 14076
PDP 4544
LP 1724
Karamar hukumar Iseyin
APC 19731
PDP 6588
LP 1371
Karamar hukumar Ibarapa ta gabas
APC 10575
PDP 4800
LP 779
Karamar hukumar Saki ta gabas
APC 6414
PDP 3634
LP 1144
Karamar hukumar Ibarapa ta tsakiya
APC 10291
PDP 5169
LP 726
Na tabbata Tinubu da yan takarar APC ne za su yi nasara, Shugaba Buhari
A wani labarin, mun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna karfin gwiwar cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyarsa ta APC, Asiwaju Bola Tinubu da sauran masu neman takara a jam'iyyarsu ne za su yi nasara.
Buhari ya tabbatar da hakan ne bayan ya kada kuri'arsa a zaben shugaban kasa da ta gudana a ranar Asabar, 15 ga watan Fabrairu, a mazabarsa da ke mahaifarsa ta Daura, a jihar Katsina.
Asali: Legit.ng