Zaben 2023: PDP Za Ta Karbi Sakamakon Zabe Da Zuciya Daya - Tambuwal

Zaben 2023: PDP Za Ta Karbi Sakamakon Zabe Da Zuciya Daya - Tambuwal

  • Gwamna Aminu Tambuwal ya magantu a kan tsarin gudanar da zaben shugaban kasa na ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu
  • Tambuwal ya ce PDP za ta karbi sakamakon zaben a duk yadda ya zo domin Allah ne ke bayar da mulki ga wanda ya so
  • A yau Lahadi, 26 ga watan Fabrairu ne hukumar zabe ta INEC za ta fara tattara sakamakon zaben a hukumance

Sokoto - Gwamnan jihar Sokoto kuma darakta janar na kwamitin yakin neman zaben shugabanm kasa na PDP, Aminu Tambuwal, ya ce jam'iyyar za ta karbi sakamakon zaben da zuciya daya.

Tambuwal wanda ya yi magana a karamar hukumar Tambuwal a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu, ya ce PDP ta yarda da bin tsari, jaridar The Nation ta rahoto.

Aminu Tambuwal yana murmushi a zaune
Zaben 2023: PDP Za Ta Karbi Sakamakon Zabe Da Zuciya Daya - Tambuwal Hoto: Aminu Waziri Tambuwal
Asali: Facebook

Ya ce:

Kara karanta wannan

Assha: EFCC ta kame daraktan kamfen gwamnan PDP na Arewa da kudade a hanyar zuwa zabe

"Mun yarda cewa Allah ne ke tsara kaddarar kowani dan Adam kuma Allah ne ke bayar da mulki ga wanda ya so.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Bugu da kari, daga bayanan da muke samu, zaben zai kasance cikin lumana ba tare da kowani tashin hankali ba.
"Wannan na nuna cewa mutane sun shirya sosai kuma sun jajirce don zaben shugabannin da suke so, wanda shine manufarmu da hangen PDP."

Hukumomin tsaro sun nuna kishin kasa yayin zabe, Tambuwal

Kan tsaro, gwamnan ya yaba ma tsarin a jihar, yana mai cewa hukumomin tsaro sun nuna kishin kasa wajen ganin nasara a tsarin.

Ya yi kira ga mutane da su ci gaba da bin doka kasancewar kasar na bukatar zaman lafiya don cimma nasara, rahoton Vanguard.

Tambuwal ya kuma yadda da yadda masu zabe suka fito don kada kuri'a, yana mai cewa tsarin akwai karfafa gwiwa sosai.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan daba sun sace na'urar aikin zabe a jihar su Buhari da kuma wata jihar

Primate Ayodele ya fadi wanda zai ci zaben shugaban kasa

A wani labarin, Primate Elijah Ayodele, babban faston Najeriya ya ayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam''iyyar Peopeles Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar ne zai lashe zaben shugaban kasa.

Primate Ayodele ya yi ikirarin cewa Allah ya nuna masa Atiku a matsayin shugaban Najeriya na gaba domin a cewarsa akwai babban aiki da Ubangiji ke so ya yi masa na farfafado da gaskiya.

Sai dai ya gargadi dan takarar na PDP da kada ya yarda ya wuce shekaru hudu kan mulki idan ya ci zabe ko ya gamu da fushin Ubangiji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng