An Ragargaji Atiku Abubakar da Bola Tinubu a Akwati 10 a Cikin Fadar Shugaban kasa
- Akwatin zaben fadar shugaban kasa watau Aso Rock sun fada hannun Peter Obi na jam’iyyar LP
- Jam’iyyar hamayya ta LP ta doke Asiwaju Bola Tinubu da Atiku Abubakar a rumfunan zabe 10
- Akwai kuri’ar da Wazirin Adamawa bai samu ko da kuri’a ko daya ba, da alama APC ce ta zo ta biyu
Abuja - ‘Dan takaran kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar adawa ta LP, Peter Obi ya samu galaba a duka akwatun goma da ke fadar Aso Rock.
Rahotanni daga Daily Trust sun tabbatar da cewa Peter Obi ya doke Asiwaju Bola Tinubu wanda ya tsaya a APC da ‘dan takaran PDP, Atiku Abubakar.
Bisa dukkan alamu ba a maganar Rabiu Kwankwaso da jam’iyyar PDP a babban birnin tarayya na Abuja.
Ga yadda sakamakon ya kasance kamar yadda The Cable ta fitar da rahoto. Za a fahimci cewa akwai rumfar da jam’iyyar PDP ba ta da kuri’a ko daya.
PU 121:
APC – 31
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PDP – 32
LP – 58
PU – 131
APC – 6
PDP – 3
LP – 17
PU 130
APC – 26
PDP – 24
LP – 113
PU – 126
LP – 42
APC – 11
PDP – 12
PU – 128
LP – 12
APC – 1
PDP – 0
PU – 122
LP – 105
PDP – 16
APC – 29
PU – 06
LP – 8
APC – 5
PDP – 2
PU – 123
LP – 86
APC – 44
PDP – 21
PU – 021
LP – 194
APC – 94
PDP – 70
PU 022
APC – 71
PDP – 78
LP – 174
" Ban yi mamaki ba "- Masoyin Atiku
Rahotanni sun ce wakilan jam’iyyu sun rika sayawa masu zabe ruwa da lemu da kayan kwalama.
Abdullahi Jalo wani matashi ne da yake kaunar Atiku Abubakar, ya shaida mani cewa bai yi mamaki da sakamakon zaben da yake gani daga Abuja ba.
Jalo yake cewa duk da haka yana sa ran ‘dan takaransa watau Alhaji Atiku Abubakar zai tabuka abin kirki a wurare irinsu Kuje, Gwagwalada da Bwari.
Zuwa yanzu duka sakamakon zaben bai fito ba, amma matashin mai zama a jihar Yobe ya ce sam bai yi mamaki yadda LP ta samu kuri’un Legas ba.
LP ta tabuka abin kirki a Legas
A wani rahoton da muka samu daga Daily Trust dazu, an ji an samu rashin gaggarwa kai kayan zabe a wasu da-dama daga cikin yankunan Legas.
Haka zalika akwai inda rikici ya barke a wajen zaben, musamman wuraren da bare suka fi yawa. Amma a sauran yankuna, zabe ya tafi lafiya kalau.
Sakamakon da ake samu har zuwa yanzu, ya nuna Bola Ahmed Tinubu yake kan gaba, yayin da Peter Obi yake na biyu, Atiku Abubakar shi ne na uku.
Legit.ng Hausa ta na da labarin kokarin LP a Ijomu, Isuwa Isale Ilobu, Ajara Badagry, da Ikorodu. Vanguard ta ce akwai inda Obi ya lashe a Alimosho.
Asali: Legit.ng