Rikici Ya Barke Tsakanin Magoya Bayan NNPP da APC a Jihar Kano

Rikici Ya Barke Tsakanin Magoya Bayan NNPP da APC a Jihar Kano

  • Rikici ya balle tsakanin magoya bayan jam'iyyar APC mai mulki da NNPP mai kayan marmari a jihar Kano
  • Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a gundumar Chiranci da ke yankin karamar hukumar Gwale
  • Jami'an tsaro sun yi iya bakin kokarin don kwantar da tarzomar amma ta kai ga sun nemi ƙarin dakaru

Kano - An shiga yanayin tashin hankali a kauyen Chiranci dake karamar hukumar Gwale a jihar Kano yayin da faɗa ya barke tsakanin magoya bayan jam'iyyar APC da NNPP..

Rahotanni sun bayyana cewa magoya bayan manyan jam'iyyin biyu sun riƙa kaiwa junansu hari yau Asabar ranar zaɓen shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya.

Gwamna Ganduje da Kwankwaso.
Rikici Ya Barke Tsakanin Magoya Bayan NNPP da APC a Jihar Kano Hoto: Ganduje da Kwankwaso.
Asali: UGC

Daily Trust ta tattaro cewa Chiranci na ɗaya daga cikin gundumomi masu ruɗani da rikitarwa kasancewarta gundumar shugaban APC na jiha, Abdullahi Abbas, da Abba Kabir Yusuf, ɗan takarar gwamna na NNPP.

Kara karanta wannan

Mutuwa Rigar Kowa: Wata Mata Mai Juna Biyu Ta Yanke Jiki, Ta Rasu a Layin Zabe a Zamfara

Gundumar ta koma filin dambarwa a lokacin zaben 2019 da ya gabata yayin da manyan kusoshin siyasar biyu zasu kaɗa kuri'unsu a rumfa ɗaya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amma a halin yanzu, hukumar zabe ta kasa (INEC) ta raba wa jiga-jigan akwatu, inda ta maida Abba Gida-Gida da iyalansa zuwa sabuwar rumfar da ta kirkira, kilo mita kaɗan daga tsohuwar.

Sabon fada ya kaure bayan faɗin sakamako

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa sabon rikicin ya soma ne jim kaɗan bayan Malaman zaɓe sun bayyana sakamakon mazaɓar shugaban APC na jihar Kano.

Rikicin ya kara yaɗuwa da tsananta bayan wasu rumfuna huɗu a yankin sun kammala kidaya kuri'u, wasu ma har sun rattaba hannun kan takardar sakamakon.

Duk da har yanzun babu wanda ya san makasudin faɗan, jami'an yan sanda, Sibil Difensa da wasu hukumomin tsaro na ci gaba da kokarin shawo kan lamarin.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Tashi da Kuri’a 1 Kacal Yayin da Atiku Ya Kawowa PDP Akwatinsa

Wani mamban NNPP mazaunin Kano, Malam Sa'idu, ya tabbatar wa Legit.ng Hausa faruwar lamarin, ya ce faɗan ya samu asali ne ganin APC zata sha kaye a Akwatun.

Yayin hira da wakilinmu da wayar tarho, Saidu ya ce Abdullahi Abbas ne fara kokarin wargaza zaben amma Sojoji da sauran jami'an tsaro suka shiga tsakani.

"Sun ga zasu faɗi ne suka tayar da rikici, har marin jami'in tsaro Abdullahi Abbas (shughaan APC na Kano) ya yi shiyasa suka tafi da shi a wurin, amma an shawo kan komai daga baya," inji shi.

Game da ɗan takarar shugaban kasa na NNPP kuwa, Malam Sa'idu, ya ce suna Addu'a Allah ya ba wanda zai zame wa Najeriya da yan Najeriya Alheri kuma ba su cire rai daga nasara ba.

A wani labarin kuma Yan Sanda Sun Cafke Mutum 15 A Katsina Kan Zargin Canja Alkalluman Zabe

Jami'in hulda da jama'an na rundunar yan sanda jihar, SP Gambo Isa, wamda ya tabbatar da lamarin, ya ce an damƙe wadanda ake zargi da na'ura mai kwakwalwa.

Kara karanta wannan

Karin bayani: INEC ta dage zaben shugaban kasa a rumfuna 141 na wata jiha

A cewarsa sun tsare da mutanen da ake zargi kuma jami'an sun ci gaba da bincike kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262