Zaben 2023: A Ƙarshe Wike Ya Kaɗa Ƙuri'arsa Bayan Jinkiri Saboda Matsalar Na'urar BVAS
- Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike da matarsa Mai shari'a Suzzette Eberechi sun isa akwatin zabensu don kada kuri'a a zaben yau Asabar 25 ga watan Fabrairu
- Sai dai Wike da matarsa ba su iya samun daman kada kuri'arsu ba domin na'urar tantance masu zabe na BVAS ta gaza tantance su duk da tsawon lokaci da aka dauka ana gwada wa
- Daga bisani jami'ar zabe ta bukaci gwamnan da matarsa su yi hakuri su tafi su dawo yayin da za ta kira jami'ai masu gyara su duba lafiyar na'urar, lamarin ya bata wa Wike rai
Jihar Rivers - Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya nuna rashin dadin sa da yadda na'urar BVAS da Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta kai akwatin zabensa ke bada matsala, Channels TV ta rahoto.
Wike ya isa akwatin zabensa na unit 7 a mazabar 9 ta karamar hukumar Obio/Akpor tare da matarsa mai shari'a Suzzette Eberechi Wike misalin karfe 10.30 na safe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma, na'urara tantance masu zabe na BVAS ba ta tantance gwamnan da matarsa ba kasancewarsu mutanen farko da za su fara kada kuri'a.
Bayan kimanin minti 20 ana gwada tantancewar, wata jami'ar zabe ta roki gwamnan da iyalansa su tafi su dawo anjima.
Ta ce jami'ai masu gyara za su duba na'urar su warware matsalar. Ta ce ana samun irin wannan matsalar a wasu sassan Rivers.
Da ya ke nazari kan yadda zaben ke tafiya bayan jira na tsawon lokaci, Wike ya bayyana zaben a matsayin abin da bai yi nasara ba.
Ya ce ya yi takaici da yadda na'uarar zaben ba ya aiki.
Yanzu-Yanzu: "Kowane Ɗan Najeriya Zai Kaɗa Kuri'u Idan Ya Yi Abu 1" INEC Ta Yi Jawabi Ana Tsaka da Zabe
Gwamnan ya kuma bayyana fargaba cewa rashin aikin da na'aurar ke yi zai iya kawo matsala ga zaben.
Sai dai daga karshe an gyara na'urar ta mazabar Wike kuma ya samu nasarar kada kuri'arsa kamar yadda Channels TV ta rahoto.
Dan majalisar tarayyar PDP a Jihar Imo ya tsallake rijiya da baya bayan kai masa hari da aka yi
A wani rahoton daban, jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a jihar Imo ta ce tana cikin damuwa bisa barazana da ake yi wa dan takararta na sanata, Hon. Uju Kingsley Chima.
Collinsa Opurozor, sakataren watsa labarai na jam'iyyar PDP a jihar Imo, cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce sau biyu aka kai wa dan takarar majalisar nasu hari a ranar Juma'a 24 ga watan Janairu.
Jam'iyyar ta PDP ta kuma ce har yanzu ma maharan ba su kyalle dan majalisar ba domin akwai motoccin yaki da aka girke a gaban gidansa.
Asali: Legit.ng