Tashin Hankali A Imo Yayin Da Dan Majalisar PDP Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Wani Farmaki

Tashin Hankali A Imo Yayin Da Dan Majalisar PDP Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Wani Farmaki

  • A ranar zabe, Asabar, 25 ga watan Fabrairu, dan majalisar wakilai na tarayya na jam'iyyar PDP ya yi sabon korafi
  • Honarabul Uju Kingsley Chima ya yi ikirarin cewa rayuwarsa na cikin babban hatsari bayan yunkurin kashe shi da wasu yan bindiga suka yi a jihar
  • Wannan bayanin ya fito ne a cikin wata sanarwa da sakataren watsa labarai na PDP a jihar Imo, Collins Opurozor ya fitar

Jihar Imo - Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a jihar Imo ta bayyana damuwa matuka kan ran daya cikin dan takarar ta a jihar Imo.

Hakan na zuwa ne a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu, yayin da dan takarar ya koka kan cewa wasu yan bindiga a jihar sun yi yunkurin halaka mamba na majalisar wakilai na tarayyya mai wakiltar Ohaji-Egbema, Oguta da Oru West, Honarabul Uju Kingsley Chima, The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da Dumi-duminsa: Shugaban Jam'iyyar PDP Na Abuja Ya Mutu a Ranar Zabe

Dan Majalisar PDP
PDP ta koka kan barazana da ta ce ana yi wa dan takararta. Hoto: Photo credit: Hon. Uju Kingsley Chima, PDP
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Chima kuma shine dan takarar jam'iyyar PDP na mazabar a zaben yau, Asabar, 25 ga watan Fabrairu.

Sanarwa da sakataren watsa labarai na PDP a jihar Imo, Collinsa Opurozor ya fitar ta ce ya tsallake rijiya da baya sau biyu a harin da aka kawo masa a daren Juma'a, 24 ga watan Fabrairu.

"Jam'iyyar mu na son sanar da yan Najeriya cewa a cikin kwana uku da suka gabata, dan takarar mu ya tsallake rijiya da baya a farmaki biyu da aka kai masa. A yayin da ya ke kammala kamfen dinsa a Umuapu a Ohaji-Egbema, kwana uku da suka shude, wasu yan ta'adda sun iso wurin sun kai wa dan takarar mu hari, har da mambobin jam'iyya da mutanen Imo.
"Har yanzu, hare-haren bai tsaya ba, domin akwai motar yaki a kofar gidansa kuma yan ta'addan suna cin karensu ba babbaka. Hakan na faruwa a jihar Imo a ranar zabe!."

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel