Kai Tsaye: Zaben Shugaban Kasar Najeriya 2023, Yadda Yake Gudana
'Rana bata karya'
Allah ya kawo mu ranar zaben shugaban kasar Najeriya 2023 inda yan Najeriya ke zaben wanda zai ja ragamar mulkin kasar daga 2023 zuwa 2027.
Yan takara 18 ne zasu fafata a wannan zabe kuma mutum milyan 87 da suka karbi katunan zabensu ake sa ran zasu fito ka'da kuria, bisa alkaluman INEC.
Sojoji da yan sanda sun isa makarantar firamare ta LEA, Lugbe
Sojoji da yan sanda sun isa makarantar firamare ta LEA da ke Lugbe, babban birnin tarayya don kwantar da tarzoman da ya barke tsakanin masu zabe da jami’an INEC.
An gano jami'an tsaron tsattsaye a wurare yayin da suka faka motarsu.
Rikici ya kaure a makarantar Firamare ta LEA, Lugbe
Rikici ya kaure a rumfar zabe ta makarantar firamare ta LEA da ke Lugbe, babban birnin tarayya Abuja.
Masu zabe sun lakadawa jami’an INEC duka kan zarginsu da dangwala kuri’u da fadawa masu zabe cewa babu takardar zabe.
Abdulsalami ya sauke hakkinsa
Tsohon shugaban ƙasa a zamanin mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar, tare da matarsa da iyalan gidansa sun kaɗa kuri'unsu a mazaɓarsu.
Gwamna Ganduje ya kaɗa kuri'arsa
Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kaɗa kuri'arsa a mazaɓar Ganduje, ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano.
Jama’a sun fito zabe sosai a rumfar zabe na fadar shugaban kasa
Dandazon jama’a sun yi tururuwan fitowa a rumfar zabe ta PU 022 da ke fadar shugaban kasa domin aiwatar da yancinsu na yan kasa.
Akwai matsala a jihar Kaduna, rumfuna da dama babu takardun zabe
Situation Room, gamayyar kungiyoyin fafutuka masu bibiyar zabe sun bayyana cewa akwai rumfuna da dama da har yanzu ba'a fara kada kuri'a ba.
A PU 02 da 03 dake unguwar Shanu, karamar hukumar Kaduna ta arewa, babu takardun zabe gaba daya.
Mai Martaba Sarkin Zazzau Ya Kada Kuri'arsa
Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Bamalli, ya kada kuri'arsa a rumfar zaben dake wajen fadar Zazzau, rahoton Leadership.
Jonathan da matarsa sun kaɗa kuri'a
Tsohon shugaban Najeriya, Dakta Goodluck Ebele Jonathan, tare da matarsa sun kaɗa kuri'unsu a Unit 39, Ward 13, Otuake, ƙaramar hukumar Ogbia a jihar Bayelsa.
Ministan sadarwa, Isa Pantami, ya kada kuri'arsa
Ministan sadarwar Najeriya kuma shehin malamin addinin Musulunci, Farfesa Isa Ibrahim Pantami, ya kada kuri'arsa yau Asabar.
Pantami wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita ya yiwa Najeriya addu'a.
Yace:
"Allah ya taimaki kasarmu, Najeriya."
Shugaban majalisar dattawa ya kada kuri’arsa
Shugaban majalisar dattawa, Lawan Ahmad ya bi sahun daukacin al’ummar Najeriya wajen kada kuri’arsa a mazabarsa da ke garin Gashua, jihar Yobe.
Osinbajo ya jefa kuri'a
Mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya kaɗa kuri'arsa a mazabarsa da ke Unit 14, Ward 1, ƙaramar hukumar Ikenne, jihar Ogun.
Osinbajo, wanda ya isa wurin tare da mai ɗakinsa ya yaba da yadda zaben ke tafiya a jihar Ogun cikin kwanciyar hankali.
Jami’an zabe na wucin gadi sun yi zanga-zanga kan rashin biyansu alawus
Jami’an INEC na wucin gadi sun gudanar da zanga-zanga kan rashin biyansu alawus dinsu a yankin Dorayi, karamar hukumar Gwale da ke jihar Kano.
Ma’aikatan sun ayyana cewa ba za su yi aikin zabe ba idan har ba’a biyasu hakkinsu ba.
Kwankwaso ya kaɗa kuri'arsa
Tsohon gwamnan Kano kuma mai neman zama shugaban ƙasa a inuwar jam'iyar NNPP mai kayan marmari, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, ya kaɗa kuri'arsa.
Mutane sun yi cirko-cirko a mazaba babu kayan zabe
Mutane sun yi cirko-cirko suna jiran tsammani, ba kayan zaɓe kuma babu jami'an hukumar zaɓe a rumfar Federal Low-Cost da ke gundumar Ɗan Iya Hardo, jihar Bauchi.
Dattijuwa a Kwankwaso tace Allah ya bamu Shugaba Na Gari Albarkan Annabi Muhammadu (SAW)
Wata dattijuwa ta fito a garin Kwankwaso domin ka'da kuri'arta.
Dattijuwar mai suna Binta Yusuf ta bayyana Aminiya cewa Allah ya bamu shugaba Nagari.
Kalli bidiyon:
An fara zabe a yankin Matazu, jihar Katsina
An fara kada kuri’u a yankin karamar hukumar Matazu da ke jihar Katsina duk da cewar mutane yan kadan ne suka fito domin aiwatar da yancinsu na yan kasa.
Gwamna Nasir El-Rufai ya bi layi a rumfar zabensa
Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-rufai ya bi sahun sauran jama’ar mazabarsa wajen yin layi don kada kuri’a a rumfar zabensa da ke Ungwan Sarki, jihar Kaduna.
Shugaba Muhammadu Buhari ya kada kuri'arsa
Shugaba Muhammadu Buhari tare da uwargidarsa, Aisha Muhammadu Buhari sun kada kuri'arsu a mazabarsu dake garin Daura, jihar Katsina.
Zaku tuna cewa Buhari ya tafi Daura ranar Juma'a tare da iyalinsa don zabe.
Bola Tinubu ya isa rumfar zabensa
Ko'ina ya kaure da hayaniya yayin da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ya isa mazabarsa. Jami'an tsaro sun mamaye koina yayin da Tinubu ke kokarin kada kuri'arsa.
Peter Obi ya isa rumfar zabensa
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi ya isa mazabarsa domin kada kuri’arsa a zaben da ke gudana a yau Asabar.
Yayin da yake zantawa da manema labarai a rumfar zabensa ta 019, Umudimakasi Square, Agulu, jihar Anambra, Obi ya nuna yakinin cewa shine zai yi nasara a zaben shugaban kasar.
An tsaurara tsaro a mazabar Kwankwaso
An ƙara tsaurara tsaron a mazaɓar dan takarar shugaban kasa a inuwar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso. Har zuwa karfe 10:08 tsohon gwamnan Kano bai isa rumfar zaben ba.
Diyar Tinubu ta isa rumfar zaben mahaifinta
Diyar Tinubu, Folashade Tinubu ta isa rumfar zaben mahaifinta kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu don kada kuri’arta.
Okowa da matarsa sun dira rumfar zabe
Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP kuma gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, tare mai ɗakinsa, Dame Edith Okowa, sun isa rumfar zaɓe Unit 14, Makarantar Firamaren Eghoma.
Jami’in INEC ya kwashi kayan zabe kan babur
A yankin Gadan Maiwa da ke karamar hukumar Ningi ta jihar Bauchi, an gano jami'in zabe kan hanyarsu ta tafiya wajen aikinsu dauke da wasu kayayyakin zabe a kan babur.
Matar Bola Tinubu ta kaɗa kuri'a
Mai dakin dan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar APC mai mulki, Oluremi Tinubu, ta kaɗa kuri'arta a Falomo, jihar Legas.
Atiku Abubakar Ya Dira Rumfar Zabensa Don Ka'da Kuri'arsa
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP ya isa rumfar zabensa don kada kuri'arsa.
Tsohon mataimakin shugaban kasan ya ka'da kuri'arsa a mazabarsa dake Jimeta.
Jami'an EFCC sun dira mazabar Tinubu
Jami'an hukumar yaki da rashawa ta EFCC sun dira rumfar zaben dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu.
An fara kada kuri’a a mazabar Kwankwaso
An fara tantancewa tare da kada kuri’a a mazabar kwankwaso rumfar zabe ta 001.
Mutane sun hau layi a rumfar zaɓen Kwankwaso
Tuni dai mutane suka hau layi a rumfar da ɗan takarar shugaban kasa na NNPP, Abiu Musa Kwankwaso, ke kaɗa kuri'a amma har yanzun ba'a manna sunayen mutane ba.
Jami'an hukumar zabe INEC da jami'an tsaro na wurin da misalin karfe 8:35 na safe.
Direbobi sun ki kai ma'akatan INEC wajen zabe saboda ba'a biyasu kudi ba
A birnin Ikeja jihar Legas, kawo karfe 8:30. direbobi sun ki kai ma'aikatan INEC rumfar zabensu.
Sun bayyana cewa sai an biyasu kudinsu zasu kai jami'an tare da kayan aiki.
An tsaurara matakan tsaro a mazabar Buhari da ke Daura
Jami’an INEC, ma’aikatan zabe na wucin gadi, jami’an ICPC, jami’an tsaro da sauransu suna nan a kasa a mazabar Shugaba Buhari da ke Daura yayin da ake shirin fara tantance masu zabe kamar yadda Channels Tv ta rahoto.
Masu zabe sun fara tururuwan fitowa a Ado-Ekiti
Mutane sun fara isa rumfunan zabensu don aiwatar da yancinsu na yan kasa a yankin Ado-Ekiti.
An gano masu zabe suna duba sunayensu a rumfar zabe ta Unit 9, Ward 11, Ado-Ekiti, jihar Ekiti.
Komai ya kankama a rumfar zaben Kwankwaso
Mutane sun fito rumfar zaben GGSS Kwankwaso, karamar hukumar Madobi inda dan takarar shugaban kasan jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso zai kada kuri'arsa.
Jami’an zabe sun fara shirya kayan zabe a mazabar Shugaba Buhari
Tun da misalin 7:57 na safe, jami’an zabe suka fara shirya wajen zabe a Baba Tone quarters da ke Waziri road, Sarkin Yara, Daura, jihar Kastsina.
Ana sa ran Shugaban kasa Muhammadu zai isa mazabar tasa da misalin karfe 9:30 domin ya kada kuri’arsa.
Jami'ai sun fara isa rumfunan zabe
Kayayyakin zaɓe sun isa rumfar da gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ke kaɗa kuri'a watau PU OO4, gunduma ta 004, ƙaramar hukumar Ekiti ta yamma.
Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng
Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng