Cikakken Tarihin Bola Tinubu: Shekarunsa, Dukiyarsa, Ƴaƴansa, Matarsa, Mahaifyarsa, Gidajensa Da Motocci
Bola Tinubu fitaccen dan siyasan Najeriya ne, jagoran kasa kuma akanta. Ya yi wa kasarsa aiki ta hanyar rike mukaman siyasa daban-daban. Tinubu shine tsohon gwamnan jihar Legas. Ya yi mulki wa'adi biyu tsakanin Mayun 1999 zuwa Mayun 2007.
Bola muhimmin dan siyasa ne kuma jagoran kasa a Najeriya. Shi mamba ne na jam'iyyar All Progressives Congress, APC. Yana kuma da sarauta na Asiwaju na Legas da Jagaban na masarautar Borgu.
Takaitaccen Bayani
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Cikaken Suna | Bola Ahmed Adekunle Tinubu |
Sunar da ya yi fice da shi | Bola Tinubu da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu |
Jinsi | Namiji |
Ranar Haihuwa | 29 ga watan Maris na 1952 |
Alamar taurari | Aries |
Garin haihuwa | Jihar Osun, Najeriya |
Mahaifiya | Abibatu Mogaji |
Shekaru | 70 (a Janairun 2023) |
Kasa | Dan Najeriya |
Kabila | Dan Afirka |
Addini | Musulunci |
Sana'a | Dan siyasa, Jagoran kasa, Akanta |
Makarantar Firamare | St John Primary School Legas da Childrens Home School, Ibadan |
Sakandare | Richard J Daley College, Chicago, Illinois, USA |
Jami'a | Jami'ar Jihar Chicago, Illinois, USA |
Shaidar Karatu | Digiri a kimiyyar aikin Akanta |
Shekarar gama karatu | 1979 |
Matsayin aure | Yana da aure |
Mata | Oluremi Tinubu |
'Ya'ya | 4 |
Fitaccen dan uwa | Attorney Adewale Tinubu |
Dukiya | Dalla Biliyan 4 |
@officialasiwajubat | |
@officialabat | |
Shafin intanet | www.bolatinubu.com |
Karin Bayani: Bidiyo Ya Fito Yayin Da Mutane Ke Yi Wa Sarkin Kano Ihu A Wurin Rantsar Da Abba Gida Gida
Tarihin Bola Tinubu
Bola bai bada wani bayani ba dangane da mahaifinsa ko yan uwansa. Mahaifiyarsa, Abibatu Mogaji, ta rasu a ranar 15 ga watan Yunin 2014 tana da shekara 68. Mahaifiyar Bola yar kasuwa ce kuma daga bisani ta zama 'Maman Kasuwa (Iyaloja) na Legas.'
Menene ainihun sunan Bola Tinubu?
An haifi Bola ne a ranar 29 ga watan Maris a 1952 a jihar Osun, Najeriya, cikaken sunansa Bola Ahmed Adekunle Tinubu.
Shekarun Bola Ahmed Tinubu nawa?
Shekarun Bola Tinubu 70 a Janairun 2023.
Karatunsa
Bola ya yi karatun frimari a St John Primary School a Aroloya, Jihar Legas, daga bisani ya koma makarantar Childrens Home a Ibadan. A 1975, Bola Tinubu ya tafi Amurka, inda ya shiga makarantar Richard J College a Chicago, Illinois.
Bayan kammala high school 'babban sakandare' ya shiga Jami'ar Jihar Chicago. Bola ya samu digiri a bangaren kararun Akanta a 1979.
Aikin da Tinubu ya yi a matsayin akanta
Ya yi wa kamfanoni da dama aiki a matsayin akanta, wasu daga cikinsu sune:
- Arthur Anderson Limited Liability Partnership
- Deloitte, Hasins & Sells
- GTE Services Corporation
Bayan aiki a Amurka na shekaru, ya dawo Najeriya a 1983. Bola Tinubu ya fara aiki da Mobil Nigeria, bayan dan lokaci aka nada shi shugaba.
Yadda Tinubu ya fara siyasa
Bola ya fara siyasa a 1992. Ya shiga jam'iyyar Social Democratic Party, SDP, daya cikin manyan jam'iyyun a wancan lokacin. An zabi shi a matsayin dan majalisar Legas ta Yamma a majalisar dattawa a jamhuriya ta uku wacce bata dade ba.
Bayan soke zaben June 12 a 1993, ya zama daya cikin wadanda suka kafa National Democratic Coalition. Kungiyar ta yi fafutikan dawo da demokradiyya kuma ta amince da Moshood Abiola a matsayin wanda ya lashe zaben June 12.
Bayan juyin mulki na 1993 a watan Nuwamba da Sani Abacha ya jagoranta, Tinubu ya yi gudun hijirar dole. Ya dawo Najeriya a 1998 bayan mutuwar Abacha. A Janairun 1999, ya yi takarar gwamna a Legas a jam'iyyar AD. An zabe shi gwamna.
Wasu cikin nasarorin gwamnatin Bola Tinubu a matsayin gwamnan Legas
- Ya fara aiki a matsayin gwamna a 1999. A wa'adinsa na farko ya yi wannan ayyukan.
- Ya samarwa marasa karfi gidaje 10,000.
- Ya saka hannun jari sosai a bangaren ilimi a Legas.
- Ya rage adadin makarantu ta hanyar mayar da su zuwa ainihin masu shi.
- Ya fara gina sabbin tituna.
A Afrilun 2003, ya sake cin zabe a matsayin gwamnan Legas. Ya kammala wa'adinsa a ranar 29 ga watan Mayun 2007.
Yana da sarautun gargajiya biyu. Shine Asiwaju na Legas don haka sunansa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Shine kuma Jagaban na masarautar Borgu a jihar Neja.
Matar Bola da yayansa
Tsohon gwamnan na Legas ya auri Oluremi Tinubu. Ita ce first lady na Legas daga 1999 zuwa 2007. Yanzu ita ce sanata mai wakiltar Legas central.
Yaran Bola Tinubu
Oluremi da Bola Tinubu suna da yara hudu. Folashade Tinubu-Ojo, Oluwaseyi Tinubu, Abibat Tinubu da marigayi Jide Tinubu. Yaran Tinubu suna harkar siyasa.
Gidajen Tinubu da motocinsa
Tsohon gwamnan na jihar Legas yana daya cikin mutane masu dukiya a kasar. Ana iya fahimtar hakan idan aka lura da irin gidajensa da da motocci.
A yanzu yana da katafaren gida a Bourdillon Road, Ikoyi Legas. Babu cikkaken bayani yadda cikin katafaren gidan ya ke. Yana kuma da gidaje a Ikoyi Estate Forestore da wasu gidajen. Yana da motocci a kalla 30. Wasu shi ya siya, wasu kuma abokai suka bashi kyauta.
A cikinsu akwai Land Range Rover, Prado Jeep, da sauransu. Tsohon gwamnan kuma yana da jirgin sama kirar Bombardier Global 6000 Express jet. Kudinsa ya dara dalar Amurka miliyan 75.
Dukiyar Tinubu
Dukiyar Tinubu ta kai kimanin $ 4 miliyan. Shine dan siyasa mafi arziki na biyu a Najeriya. Dukiyarsa sun hada da manyan motoccin alfarma, jirgin sama, gidaje da filaye a sassan kasar.
Me ya faru da Bola Ahmed Tinubu?
- A Yunin 2022, jam'iyyar APC ta zabe shi a matsayin dan takarar shugaban kasarta.
- Wasu abubuwa dangane da Bola Tinubu
- Ya taka muhimmin rawa a kafa jam'iyyar APC a 2013
A Janairun 2019, hukumar EFCC ta wanke shi kan zargin hadin baki, yin amfani da ofis ba bisa ka'ida ba, almundahar kudi da rashawa da ke da alaka da hannun jarin V Mobile a 2004, tare da gwamnan Akwa Ibom, Obong Victor Attah, da James Ibori na Delta.
Bola Tinubu ya goyi bayan tsare-tsaren gwamnati da jadadda siyasar cikin gida yayin gwamnatin Buhari lokacin yana shirin takara a 2023.
A 2019, ya goyi bayan tazarcen Buhari kuma ya taimaka masa ya kayar da Atiku Abubakar na PDP.
“Na Hango An Rantsar Da Shi a Matsayin Shugaban Kasa”: Fasto Ya Yi Sabon Hasashe Kan Tinubu
A bangare guda, Theophilus Olabayo, Shugaban cocin Evangelical Church of Yahweh Worldwide, ya yi hasashen cewa za a rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban Najeriya na gaba a ranar 29 ga watan Mayu.
Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, da kuri'u fiye da miliyan takwas.
Amma, wasu daga cikin yan takara da suka fafata da shi a zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu suna kotu don kallubalantar nasarar ta Tinubu bisa dalilai daban-daban da suka ce sun janyo cikas ga zaben.
Asali: Legit.ng