Shugaban Kasa: Karfi da Raunin Tinubu, Atiku, Obi, Kwankwaso a Zaben Ranar Asabar
- Bisa al’ada, zaben Najeriya ya koma tsakanin Jam’iyya mai-mulki da kuma babbar Jam’iyyar adawa
- A shekarar nan ta 2023, zaben ya sha bam-bam domin akwai manyan ‘yan takara hudu da suke neman mulki
- Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso su na harin shugabanci tare da Bola Ahmed Tinubu da Atiku Abubakar
Abuja - A wannan rahoto da muka tsakuro daga The Cable, an yi bayanin inda kowane ‘dan takaran shugaban kasa yake da karfi da inda zai samu matsala.
1. Bola Tinubu
Babban abin da zai taimakawa Bola Tinubu shi ne jam’iyyarsa ta APC ce a kan mulki, tana da Gwamnoni fiye da 20 da ke mulki a Jihohin kasar nan.
APC ta na da Sanatoci sama da 60 da ‘yan majalisar wakilan tarayya. Baya ga haka akwai Ministoci da masu rike da mukamai da za su taimaka mata.
Tinubu zai samu goyon bayan Musulman Arewa a dalilin tikitin Musulmi da Musulmi, sannan maida mulki zuwa kudu ya taimakawa takararsa.
Matsalolin da Tinubun zai samu shi ne ana zargin gwamnatin APC da jefa kasa cikin matsin lambar tattalin arziki, sannan an kawo tsarin canza kudi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Baya ga wahalar canza kudi da man fetur da ake fama da su, wasu kiristoci za su kauracewa APC a zabe mai zuwa saboda dauko Kashim Shettima da aka yi.
Akwai masu tunanin ‘dan takaran na jam’iyyar APC mai shekaru 70 bai da koshin lafiya.
2. Atiku Abubakar
Tun 1993 Atiku Abubakar yake neman mulkin Najeriya, saboda haka ya fi sauran ‘yan takaran kwarewa, kuma yana da jama’a a kowane lungu na kasar nan.
Masu nazari su na ganin Wazirin Adamawa ya fi kowa sanin makamar aiki a cikin ‘yan takaran.
Atiku zai amfana da kuri’un wadanda suka gaji da mulkin APC amma kuma tsayawa takarar Obi za ta girgiza PDP a Kudu maso Kudu da Kudu maso gabas.
Matsalar da Atiku zai samu ita ce ana maso kallon Fulani kuma Musulmi a yayin da Muhammadu Buhari daga yankin Arewa ya yi shekaru takwas a kan mulki.
3. Peter Obi
Kusan ba a taba yin ‘dan siyasar da ya samu saurin karbuwa musamman a Kudu maso gabas irin Peter Obi ba, matasa su na goyon bayan ‘dan takaran na LP.
Kiristoci a Kudu da Arewa da-dama za su zabi jam’iyyar LP ganin shi ne kadai ba Musulmi ba, kuma duk a cikin manyan ‘yan takaran 2023, shi kadai ne Ibo.
Jaridar ta The Cable ta ce a lokacin da ‘Yan kabilar Ibo za su yi farin cikin samun mulkin Najeriya, Obi ba zai yi wani farin jini ga mafi yawancin ‘Yan Arewa ba.
4. Rabiu Kwankwaso
Tsohon Gwamnan Kano yana ji da farin jini musamman a jihar Kano da makwabtanta, wannan zai taimaka masa a Arewa inda ake da yawan kuri’u.
Duk da mafi yawan jama’a su na ganin cancantar Rabiu Kwankwaso, akwai masu ra’ayin bai kamata wani mutumin Arewa ya sake karbe mulki yanzu ba.
Rashin dauko gogaggen ‘dan siyasa a matsayin abokin takara zai iya jawo kuri’un NNPP su kare a Kano, Kaduna, Jigawa, Bauchi, Gombe da kewayensu.
Duk shaharar Sanata Kwankwaso ta tsaya ne a Arewa, kalubalen da zai samu a Kudancin Najeriya zai jawo ya gagara kawo akalla kuri’u 25% a jihohi 24.
Za a raba kuri'u miliyan 87
A wani rahoto da muka fitar, kun ji cewa ko menene zai faru a zaben gobe, ana ganin Bola Tinubu zai samu kuri’u a Jihohi rututu saboda Gwamnonin APC.
An fi ganin nasara a wajen manyan ‘yan takara hudu, musamman Atiku Abubakar, Bola Tinubu da Peter Obi, da alama a karon farko, Attajiri zai ci zabe.
Asali: Legit.ng