Wike Ga Ribas: Ba Zan Muku Kuskuren Zaben Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ba
- Gwamna Wike ya ja hankalin mutanen jihar Ribas da cewa ba zai yaudare su ba game da wanda zasu zaba ranar Asabar
- Nyesom Wike, jagoran gwamnonin G-5 sun raba gari da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyarsa PDP, Atiku Abubakar
- A halin yanzun ana jiran aga wane ɗan takara mazauna Ribas zasu zaba tsakanin manyan masu neman gaje Buhari
Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya faɗawa mutanen jihar cewa su aminta da shi game da ɗan takarar shugaban kasan da zasu jefa wa kuri'unsu ranar Asabar.
Gwamnan ya jaddada cewa tuni masu ruwa da tsaki suka ɗauki wanda ya cancanta Ribas ta tula wa kuri'unta kuma sun bi matakan da ya dace wajen zaɓen.
Wike ya ce ba zai wa mutanensa zaɓen tumun dare ba kuma ya sake nanata cewa zai ci gaba da fafutukar kare muradan mazauna jihar Ribas duk rintsi kuma a ko wane lokaci.
The Nation ta rahoto cewa Nyesom Wike ya yi wannan jawabin ne yayin kaddamar da wasu muhimman ayyukan titi a yankin ƙaramar hukumar Patakwal ranar Alhamis.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A kalamansa ya ce:
"Idan ka samu dama har mutane suka ɗora yakininsu a kanka, ya zama tilas ka sanya su farin ciki, ka tabbata ka samar musu da abinda zai inganta rayuwarsu, ya gyara mahallansu kuma ya ɗaga harkokin tattalin arzikin yankinsu."
Wike ya ƙara da cewa jihar Ribas ta ba shi damarmaki da yawa a rayuwarsa kuma ya cimma nasarori da dama sannan ba zai yi ƙasa a guiwa ba wajen kare martabar jihar.
Ya ce babu wani abun duniya da za'a ba shi ya sayar da kimar jihar kamar yadda wasu suke yi domin amfanar kansu kaɗai.
"Ina da tabbacin mutanen wannan yankin ba zaku manta da wannan titin ba, idan nine ku zan dauki hoton tsohon titin Iloabuchi da sabo na maƙala a gidana, kullum da safe na kalli hoton."
- Nyesom Wike.
Bana tunanin Atiku zai kai labari ranar Asabar - Lauya
A wani labarin kuma An bayyana Babban Abinda Zai Ja Wa Atiku Faɗuwa Zaben Shugaban Kasa 2023
Wani fitaccen masanin shari'a a Najeriya ya bayyana dalilansa da ya sa yake ganin Atiku Abubakar ba zai kai labari ba a zaben ranar Asabar.
Ridwan Oyafajo, ya ce rigingimun cikin gida da suka addabi PDP da zaɓen ɗan takarar mataimkin shugaban kasa na cikin matsalolin Atiku.
Asali: Legit.ng