“Ku Garzaya Kotu Idan Ba Ku Gamsu Ba”: Buhari Ga Yan Takara Ya Yi Gargadi Kan Rikici

“Ku Garzaya Kotu Idan Ba Ku Gamsu Ba”: Buhari Ga Yan Takara Ya Yi Gargadi Kan Rikici

  • An bukaci yan takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa da su wanzar da zaman lafiya a duk yadda sakamakon zaben ya zo
  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya yi wannan rokon ne a taron yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin dukkanin yan takarar
  • Ya bayyana cewa duk dan takarar da bai gamsu da sakamakon zaben ba ya garzaya kotu

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci yan takarar da ke takara a zaben shugaban kasa da su yarda da sakamakon zaben 2023 da za a yi a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu.

Ya yi rokon ne a ranar Laraba, 22 ga watan Fabrairu, a taron sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya na kafin zabe wanda aka yi a Cibiyar taro na kasa da kasa da ke Abuja, rahoton Aminiya.

Kara karanta wannan

Abinda Shugaba Buhari Ya Faɗa Wa Tinubu, Atiku, Kwankwaso da Sauran Yan Takara a Taron Abuja

Shugaba Buhari ya tabe baki
“Ku Garzaya Kotu Idan Ba Ku Gamsu Ba”: Buhari Ga Yan Takara Ya Yi Gargadi Kan Rikici Hoto: MBuhari
Asali: Twitter

A cewar wata sanarwa da kakakinsa, Femi Adesina ya saki, Shugaba Buhari ya ce:

"Bari na tunatar da daukacin yan Najeriya cewa wannan ita ce kasa guda da muke da ita kuma ya zama dole mu yi duk mai yiwuwa don kare ta, hadin kanta da zaman lafiya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Duk dan takarar da bai gamsu ba ya bi tsarin shari'a, kuma dole mu kasance da kwarin gwiwa don yarda da tsarin shari'armu.
"Ina mai sake bukatan yan takara da su bi yarjejeniyar zaman lafiya da suka sanya hannu a kai a yau."

Ku guji rikici, ku je kotu idan baku gamsu ba - Buhari ga yan takara

Kamar yadda Channels TV ta rahoto, ya bukaci yan takarar da su guji ingiza tarzoma ko rikici yayin da aka sanar da sakamako.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Atiku, Tinubu Da Wasu Yan Takara Za Su Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya

Shugaba Buhari ya bayyana cewa duk wanda bai gamsu da sakamakon zaben ba toh su mika kokensu ga kotun da ya dace domin ayi zama.

Ya ce:

"Kada a tada tarzoma ko wani nau'i na rikici bayan sanar da sakamakon zaben. Duk wani korafi, na boye ko na sarari a muka shi kotunan da ya dace."

Buhari ya gana da shugaban hukumar INEC

A wani labarin, mun ji cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sa labule da Shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, Farfesa Yakubu Mahmoud a ranar Laraba kan zaben ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng