Jiga-Jigan PDP Sun Nemawa Atiku Kuri’un Al’ummar Jihar Lagas

Jiga-Jigan PDP Sun Nemawa Atiku Kuri’un Al’ummar Jihar Lagas

  • Jam'iyyun siyasa sun dukufa wajen tallata kansu a tsakanin al'umma yayin da ya rage yan kwanaki ayi babban zaben kasar
  • Jiga-jigan PDP a jihar Lagas sun bukaci yan Najeriya da su kada kuri'unsu ga Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa
  • Za a fafata a zaben shugaban kasa tsakanin Bola Tinubu na APC, Rabiu Kwankwaso na NNPP, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP

Lagos - Tsohon ministan hadin kan Afrika, Cif Abimbola Ogunkelu, shugaban jam'iyyar PDP a jihar Lagas, Philip Aivodji; tsohon siyaman din jam'iyyar a jihar, Tunji Selleh sun bukaci masu zabe da su zabi Atiku Abubakar a zaben ranar Asabar.

Jiga-jigan jam'iyyar sun bukaci hakan a babban taron PDP na jihar wanda ya gudana a sakatariyar jam'iyyar da ke Lagas.

Dan takarar shugaban kasa na PDP da mataimakinsa tsaye suna jawabi
Jiga-Jigan PDP Sun Nemawa Atiku Kuri’un Al’ummar Jihar Lagas Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Sun kuma bukaci yan Najeriya da su fito kwansu da kwarkwatarsu don zaben Atiku kuma cewa kada su yarda wani ya tsorata su daga wajen sauke yancinsu na yan kasa, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Yan Kwanaki Kafin Zabe, Malaman Kano Sun Bayyana Dan Takarar Da Za Su Zaba Tsakanin Atiku Da Tinubu

A wajen taron, mambobin kwamitin uwar jam'iyya na jihar sun tarbi mambobnin kungiyar NURTW karkashin jagorancin shugabanta na kudu maso yamma Kwamrad Olusola Akingbola.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An kuma mikawa mambobin kungiyar sufurin na kasa tutar PDP a matsayin mambobin jam'iyyar.

Atiku ne ya fi cancanta cikin masu tseren shugabancin kasa, Kungiyar matasa na YGM

Shugabannin kungiyar matasa ta YGM da suka hada da Hon. Oluwadare Oyebamiji; Dr. Ayodele Elegbeleye da Ahmed Yahaya Bello (WAZOBIA) ma sun halarci taraon.

Sun bayyana Atiku a matsayin wanda ya fi cancanta cikin yan takarar da ke tseren neman kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Har ila yau, sun ce idan aka zabi Atiku a matsayin shugaban kasar Najeriya na gaba, zai ceto kasar daga fadawa cikin rudani.

Ogunkelu, wanda ya kasance mamba a kwamitin amintattu na PDP, ya jinjinawa jiga-jigai da mambobin jam'iyyar kan jajircewarsu wajen aiki don nasarar Atiku.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar NNPP a Kano Tace Jami'an Na Kai Musu Hare-Hare Ofishin Kamfe

Ya ayyana cewa za a zabi Atiku a zaben ranar Asabar a matsayin shugaban kasa na gaba, yana mai rokon yan Najeriya da su yi zabe da babban yatsarsu don kuri'unsu ya yi tasiri, rahoton Nigerian Tribune.

Atiku za mu zaba saboda tikitin Musulmi da Kirista, Kungiyar malaman Kano

A wani labarin, yan kwanaki kafin babban zaben 2023, kungiyar malaman jihar Kano sun ayyana goyon bayansu ga dan tyakarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

Kungiyar da ta hada da mabiya darikar Tijjaniyya, Izala, Qadiriyya da sauransu ta ce Atiku ne ya fi cancanta da shugabancin Najeriya kasancewar ya riki mukamin mataimakin shugaban kasa a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng