Ba na Goyon Bayan Tinubu Inji Daya Daga cikin Gwamnonin PDP da ke Fada da Atiku
- Dr. Okezie Ikpeazu ya maida raddi ga tsohon Gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu a kan 2023
- Gwamnan na Abia ya nuna babu abin da ya hada shi takarar Bola Tinubu a zaben shugaban kasa
- Sanata Orji Uzor Kalu ya lissafo Gwamnan a cikin wadanda za su taimakawa ‘dan takaran APC
Abia - Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu ya musanya zargin da ake yi masa na goyon bayan ‘dan takaran jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa.
The Guardian ta rahoto Gwamna Okezie Ikpeazu yana cewa bai cikin masu marawa Bola Ahmed Tinubu baya domin ya zama shugaban Najeriya a APC.
Wannan karin haske zai zama raddi ga Sanata Orji Uzor Kalu wanda aka ji yana cewa Gwamnansa da Nyesom Wike su na tare da su a babban zabe.
Orji Uzor Kalu wanda ya yi Gwamnan Abia tsakanin 1999 zuwa 2007, yana cikin jagororin APC, kuma yana ganin Bola Tinubu zai lashe zaben 2023.
Orji Uzor Kalu ya fadi gaskiya?
Da yake yi wa manema labarai jawabi bayan an shimfida kwalta a wani titi da yake ginawa a garin Aba, Gwamnan ya fito da kuskuren da Orji Kau ya yi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar Dr. Ikpeazu, abin da Sanata Kalu ya fada tunaninsa ne da abin da yake buri. Sai dai Gwamnan bai fadi wanene ‘dan takaransa a zaben bana ba.
Daily Trust ta rahoto Okezie Ikpeazu yana cewa babu wani daga cikin Gwamnonin G5 da ya isa ya tursasa takwaransa ya goyi bayan ‘dan takarar wani.
Ikpeazu mai neman takarar Sanata a karkashin PDP ya nuna har gobe yana tare da jam’iyyar adawar, ya ce akwai wasu abubuwan da ya kamata a gyara.
Wannan shi ne abin da Darektan hulda na musamman da jama’a na kwamitin yakin neman zaben PDP a Abia, John Okiyi Kalu ya fada a wani jawabinsa.
Ikpeazu: Ba za ayi wasa da Tinubu ba
A wata hira da aka yi da Mai girma Gwamnan a jaridar The Nation, ya nuna cewa babu wanda ya isa ya raina Bola Tinubu mai neman shugabanci a APC.
Ikpeazu ya nuna ba a goyi bayan Tinubu ya samu tikitin jam’iyya mai mulkin ba, amma ya dage ya yi nasara a kan sauran abokan hamayyarsa a Yuni.
'Dan takara ya tafi kurkuku
An ji labari ’yan sandan jihar Ribas sun kai Hon. Ephraim Nwuzi a kotu saboda wasu kalamansa. Za a yi zabe ‘Dan takaran majalisar na APC yana gidan yari.
An ga wani bidiyo da ‘Dan majalisar ya fadawa magoya bayansa su aukawa mutane a lokacin yin zabe. Barista Emenike Ebete ya nemi beli amma bai dace ba.
Asali: Legit.ng