Siyan Ƙuri'a Ne Rabon Abinci Kyauta Da Gwamnatin Kaduna Ke Yi, PDP
- Jam'iyyar PDP a jihar Kaduna ta bankaɗo wani shirin gwamnatin APC na siyan ƙuri'u a jihar
- PDP tace jam'iyyar APC yaudarar mutanen jihar Kaduna take son tayi shiyasa ta bijiro musu da shirin
- Jam'iyyar tayi kiran da mutane su ankara da wannan sabuwar yaudarar da gwamnatin APC ta zo da ita
Kaduna- Jam'iyyar PDP a jihar Ƙaduna ta nuna shakkun ta kan kyautar abinci, kudin mota da duba lafiya kyauta da gwamnatin jihar ta ɓullo da shi domin rage raɗaɗin sauya fasalin takardun kuɗin naira da babban bankin Najeriya (CBN) yayi.
A cewar sakataren jam'iyyar na jihar Alhaji Ibrahim Wusono, wannan abin da gwamnatin ta ɓullo da shi wani shiri ne na siyan ƙuri'a a zaɓen 2023. Rahoton Punch
Sakataren ya kuma ƙara da cewa jam'iyyar PDP a ɗinke take babu wata ɓaraƙa a jihar, inda yace dukkanin jiga-jiganta sun ɗinke waje ɗaya domin ƙwato mulki a hannun gwamnatin APC. Rahoton Vanguard
A kalamansa:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Sun kawo shirin ɗauko mutane daga Kaduna zuwa Zaria kyauta. Ina so na janyo hankalin mutanen jihar Kaduna cewa wannan na daga cikin yaudarar da gwamnatin APC ta saba da ita ne sama da shekara bakwai da suka wuce."
"Mutane yakamata su fahimci cewa gwamnatin APC ce ta kori ma'aikata sama da 62,000 ciki har da malaman makaranta a jihar."
“Gwamnatin APC ce ta rusa gidaje, kasuwanni, sannan a ƙarƙashin ta ne mutanen jihar Kaduna ba su da kwanciyar hankali, ku dubi abinda yake faruwa a Birnin-Gwari, Giwa, Chikun da Kajuru? Ko ina cikin ɗar-ɗar suke."
“Yaudara ce kawai. Sun mulki jihar nan sama da shekara bakwai da rabi, shin sun mayar da sufuri kyauta a jihar? Ba suyi ba. Sai yanzu saboda lokacin zaɓe ne. Kuma wannan siyan ƙuri'a ne."
Kwankwaso Zai Dura Kano Domin Yin Yawon Kamfen Karshe a Yakin Zaben 2023
A wani labarin na daban kuma, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP zai dura a jihar Kano domin kammala yaƙin neman zaɓen sa.
Rabiu Musa Kwankwaso yana daga cikin ƴan takarar da zasu fafata neman kujerar shugaban ƙasa a zaɓen ranar Asabar mai zuwa.
Asali: Legit.ng