Kungiya ta Nemi Afuwar Goyon Bayan Buhari a 2015 da 2019, ta ce Atiku ne Mafita

Kungiya ta Nemi Afuwar Goyon Bayan Buhari a 2015 da 2019, ta ce Atiku ne Mafita

  • Wata kungiya ta Masoyan Shugaba Muhammadu Buhari da Yemi Osinbajo sun fice daga APC
  • Atiku Abubakar ya samu goyon bayan ‘Yan Buhari-Yemi Osinbajo Nationwide Supporters Group
  • Shugaban kungiyar, Danjuma Fachiwe Gwoza ya ce goyon bayan APC bai tsinana masu komai ba

Abuja - Wasu magoya bayan Shugaban Najeriya a karkashin inuwar Buhari-Yemi Osinbajo Nationwide Supporters Group sun canza alkibla a siyasa.

Vanguard ta rahoto cewa kungiyar ta na neman afuwar ‘Yan Najeria da ta goyi bayan gwamnatin APC a makance, wanda a cewarta ta jefa jama’a a kunci.

‘Yan kungiyar ta Buhari-Yemi Osinbajo Nationwide Supporters Group sun dawo daga rakiyar Muhammadu Buhari, su na goyon bayan Atiku Abubakar.

Mabiya wannan kungiyar sun ce a zaben sabon shugaban kasa da za ayi a ranar Asabar mai zuwa, za su goyi bayan Atiku Abubakar-Ifeanyi Okowa.

Kara karanta wannan

Sanata Ya Tona Komai, Ya Jero Manyan Gwamnonin PDP da ke Tare da Tinubu a Boye

Atiku
Atiku Abubakar a taron 'Yan PDP Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaban kungiyar ya yi magana

Shugaban tafiyar, Hon. Danjuma Fachiwe Gwoza ya bada wannan sanarwa a lokacin da ya zanta da manema labarai tare da ‘ya ‘yan kungiyarsa a Abuja.

Da yake bayani a ranar Laraba, Danjuma Fachiwe Gwoza ya ce su masoyan Muhammadu Buhari da Yemi Osinbajo sun shiga inuwar lemar PDP.

Gwoza ya ce ‘ya ‘yan kungiyarsu sun kai 9,313,846, kuma da su aka yi kokari wajen ganin Shugaba Muhammadu Buhari ya lashe zabukan 2015 da 2019.

A cikin ‘ya ‘yan kungiyar akwai matasa masu kananan kananan sana’o’i da suka ba APC gudumuwa.

"Ayi hakurin abin da muka yi"

"‘Ya ‘yan gamayyar nan su na ba ‘Yan Najeriya hakuri a kan makauniyar goyon bayan da muka ba gwamnatin APC da ta gagara cika alkawuran da ta dauka.
Tsantsagwaron gazawar da tayi ya jefa kasar nan cikin mawuyacin halin da ya fi karfin kowa."

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Dab da zabe, Tinubu ya dura a jiharsu, zai yi wani taro da shugabannin Yarbawa

- Hon. Danjuma Fachiwe Gwoza

Rahoton ya ce Gwoza ya yi amfani da damar wajen godewa irinsu Sanata Abubakar Mahdi da Raymond Dokpesi wanda manya ne a tafiyar Atiku Abubakar.

A zaben da za ayi, kungiyar ta ce tana harin nasarar Atiku/Okowa domin su na da jama’a a kowane lungu.

"Canza kudi awon igiya ne"

An ji labari Dr. Abdullahi Ganduje ya ce babu shawara ko doka, Gwamnan CBN ya canza kudin Najeriya, a cewarsa burin hakan shi ne su fadi zabe.

Gwamnan Kano ya ce tsarin fito da sababbin kudi aikin Gwamnan CBN watau Godwin Emefiele ne ba kowa ba, yana mai nesanta hakan da APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng