Zamfara: Dan Takarar Gwamnan ADC Ya Ajiye Takararsa, Ya Koma APC

Zamfara: Dan Takarar Gwamnan ADC Ya Ajiye Takararsa, Ya Koma APC

  • Dan takarar gwamnan jam’iyyar ADC a Zamfara, Ahmad Hashim, ya sauya sheka zuwa APC ana gab da zabe
  • Mataimakin gwamnan jam’iyyar YPP, Alhaji Abubakar Gandi, ma ya sauya sheka zuwa jam’iyyar mai mulki a jihar
  • Haka kuma, jam’iyyar APC a Zamfara ta tarbi masu sauya sheka daga YPP da NNPP gabannin zaben 2023

Zamfara - Jam'iyyar All Progressives Congress, APC ta yi babban kamu na yan takara daga jam'iyyun adawa a ranar Talata, 21 ga watan Fabrairu, inda suka ajiye takararsu suka koma karkashin inuwarta.

Mambobin jam'iyyun adawar da suka dawo APC sun hada da dan takarar gwamna na jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) Dr Ahmad Hashim.

Sai kuma dan takarar mataimakin gwamna na Young Progressive Party (YPP), Alhaji Abubakar Gandi, jam'iyyar PM News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan Takarar Gwamna 3 Sun Janye, Sun Ayyana Goyon Bayansu Ga Sharada a Zaben 2023

Masu sauya sheka rike da satifiket dinsu
Zamfara: Dan Takarar Gwamnan ADC Ya Ajiye Takararsa, Ya Koma APC Hoto: PM News
Asali: UGC

A cewar wata sanarwa daga kakakin APC a Zamfara, Yusuf Idris, sauran jiga-jigai da yan takarar ADC, YPP, AAC da NNPPP ma sun sauya sheka zuwa APC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Dan takarar gwamnan ADC, Dr Ahmad Hashim ya jagoranci yan takarar kujerar sanata uku, yan takarar kujerar majalisar wakilai biyar da yan takarar majalisar jiha 11 zuwa gidan gwamnati a Gusau inda suka sanar da sauya shekarsu zuwa APC.
"Yayin taron, dan takarar mataimakin gwamna na YPP, Alhaji Abubakar Gandi, dan takarar sanata na Zamfara ta yamma da shugaban karamar hukumar Talata Marafa da sakataren jam'iyyar ma sun sanar da sauya shekarsu zuwa APC."

A cewar Idris, yan takarar majalisun dokokin tarayya da na jiha a jam'iyyar, mataimakin ciyaman, sakataren jam'iyyar, Jamilu Dinawa Isah Saminu da sakataren tsare-tsare na jam'iyyar duk sun koma APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Ta Karewa Atiku, Bola Tinubu Ya Samu Gagarumin Goyon Baya a Arewa Kwana 5 Gabanin Zaben 2023

"APC ta kuma tarbi dan takarar sanatan Zamfara ta yamma na jam'iyyar African Action Congress (AAC), Hon. Bello Danda da shugaban jam'iyyar, Zulkifilu Ma’azu da sakataren karamar hukumar Talata Mafara, Huzaifa Zubairu.
"Dan takarar majalisar wakilai na jam'iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a mazabar Maru/Bungudu, Yunusa Yalbai ya sanar da sauya shekarsa ga APC.
"A jawabansu mabanbanta, masu sauya shekar sun ce sun gamsu da gwamnatin APC a jihar karkashin Gwamna Bello Matawalle wanda shine ya zaburar da shi ya koma jam'iyyar."

Za mu yi aiki da kowa - APC ga masu sauya sheka

Masu sauya shekar sun yaba ma kokarin gwamnatin jihar musamman wajen yaki da rashin tsaro.

Da yake martani, shugaban kwamitin tarban masu sauya sheka na APC, Sanata Tijjani Yahaya-Kaura ya yaba masu kan dawowa jam'iyyar da ya yi, cewa sun yanke shawarar da ta dace."

Ya kuma ba masu sauya shekar tabbacin cewa za a tafi da su a kan komai na jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Saura Kwana 5 Zabe, APC Ta Dakatar Da Mataimakin Shugabanta Saboda Rabar Gwamnan PDP Fintiri

Ya bukace su da su ci gaba da nemawa APC goyon baya a babban zabe mai zuwa a jihar da ma Najeriya.

Ku yi aiki da hankali yayin zabe, Shehu Sani ga yan Najeriya

A wani labarin, Sanata Shehu Sani ya yi kira ga yan Najeriya a kan su yi aiki da hankali sannan su duba cancanta yayin zabar shugabanni a ranar Asabar mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel