Yanzu Yanzu: APC Ta Dakatar Da Mustapha Salihu Kan Hulda Da Dan PDP

Yanzu Yanzu: APC Ta Dakatar Da Mustapha Salihu Kan Hulda Da Dan PDP

  • An dakatar da mataimakin shugaban jam’iyyar All Progressives Congress, APC, a arewa maso gabas, Mustapha Salihu
  • Kwamitin aiki na gudunmar Rumde a karamar hukumar Yola ta dakatar da Salihu na tsawon watanni shida
  • Jam’iyyar ta kuma sanar da dakatar da shugabanta na gudunmar, Abdulkadir Abdullahi

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta dakatar da Mustapha Salihu, mataimakin shugabanta na arewa maso gabas, na tsawon watanni shida kan zargin cin dunduniyar jam'iyyar.

An tattaro cewa Salihu yana hulda da Ahmadu Fintiri, gwamnan jihar Adamawa kuma mamba na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), jaridar The Cable ta rahoto.

Logon APC
Yanzu Yanzu: APC Ta Dakatar Da Mustapha Salihu Kan Hulda Da Dan PDP Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Batun dakatarwar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka saki a ranar Lahadi, 19 ga watan Fabrairu.

Sai dai kuma, shugabancin jam'iyyar a jihar ta fito ta bayyana cewar dakatar da aka yi wa Salihu bai da tasiri.

Kara karanta wannan

Yan Kwanaki Kafin Zabe: PDP Ta Hadu Da Gagarumin Cikas a Kano, Tsagin Shehu Sagagi Sun Yi Maja Da Jam’iyyar Kwankwaso

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kwamitin aiki na APC a jihar Adamawa ta bayyana dakatarwar da aka yi wa Salihu a mnatsayin wanda baya bisa ka'ida.

A wata sanarwa da ya saki a ranar Litinin, sakataren jam'iyyar a jihar, Dr. Raymond Chidama, ya ce makiyan jam'iyyar na amfani da wasu mutane wajen hargitsa damar da jam'iyyar ke da shi a zabe mai zuwa.

An dakatar shugaban APC a gudunmar Rumde

Daily Post ta rahoto cewa domin samun damar dakatar Salihu, sai shugabannin APCa gudunmar Rumde suka fara dakatar da shugabansu, Abdulkadir Abdullahi, wanda ake ganin ya hana dakatar da Salihu.

Abdullahi ya fito ya yi watsi da dakatar da shi da aka yi yana mai cewa har yanzu shine shugaban jam'iyyar a gudunmar kuma cewa Mustapha Salihu bai yi komai da za a dakatar da shi ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Muna Tare Da Gwamnoni Kan Lamarin Naira: Shugaban Uwar Jam'iyyar APC

Tsagin PDP reshen Kano sun sauya sheka zuwa NNPP

A wani labarin, mun ji cewa jam'iyyar PDP tsagin Shehu Sagagi a jihar Kano sun rushe tsarinsu a cikin jam'iyyar NNPP gabannin babban zaben kasar.

Sagagi ya ce sun fice daga PDP ne saboda rashin damokradiyya da kuma tsananin son zuciya na shugabannin jam'iyyar.

Masu sauya shekaru sun kuma nuna kwarin gwiwa cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne zai lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel