"Tikitin Muslim-Muslim Zai Hana Tinubu Zama Shugaban Ƙasa", Datti Baba-Ahmed
- Mataimakin Peter Obi ya bayyana dalilan da ya sanya ƴan Najeriya ba zasu kaɗa ƙuri'un si ga Tinubu ba
- Datti Baba-Ahmed yace dalilin da ya sanya Tinubu ya kasa zama mataimakin shugaban ƙasa a 2015 shine zai sanya ƴan Najeriya su ƙi zaɓar sa
- Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasar ya kuma bayyana cewa jam'iyyar ce zata yi nasara a jihar Tinubu
Legas- Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Datti Baba-Ahmed, yace ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu ba zai kai labari ba a zaɓen ranar Asabar.
Da yake magana yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels Tv a ranar Talata, Baba-Ahmed ya bayyana cewa Tinubu zai sha kashi ne a zaɓen saboda tikitin muslim-muslim na jam'iyyar APC. Rahoton The Cable
Yace Tinubu wanda ya kasa zama mataimakin shugaban ƙasa na shugaba Buhari a 2015, yayi kaɗan ya ƙaƙabawa ƴan Najeriya muslim-muslim a 2023.
Datti yace wannan haɗin na APC ba zai yi aiki ba a Najeriya a wannan karon.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya bayyana cewa jam'iyyar LP ce kawai take da haɗi mai kyau wanda zai sanya ta lashe zaɓen shugaban ƙasa domin ciyar da ƙasar nan gaba.
"Dalilin da ya sanya Tinubu a yanzu ba shi bane mataimakin shugaban ƙasa shine zai sanya ba zai zama shugaban ƙasa ba" Inji shi.
“Abinda ya kasa aukuwa a 2015 lokacin takarar Buhari, ba zai taɓa aukuwa ba a yanzu domin an wuce wannan lokacin."
“Ba zata taɓa yiwuwa ba a Najeriya, tikitin muslim-muslim ba zai yi aiki ba."
Datti ya kuma ƙara da cewa jam'iyyar LP, zata yi nasara a jihar Legas, duk da ƙarfin faɗa aji da Tinubu yake da shi a jihar. Rahoton Arise News
“Da yardar Allah, mun yi nasara a Legas mun gama, duk da cewa akwai Tinubu a can." Shin za su fito ne su tarwatsa mutanen dake kaɗa ƙuri'a?"
Har Yanzu Nine Sahihin Ɗan Takarar PDP", Sanata Nnamani Ya Magantu
A wani rahoton korarren ɗan takarar PDP ya bayyana gaskiya kan takarar sa a zaɓen ranar Asabar.
Asali: Legit.ng