‘Diyar Atiku ta Zama Lauyarsa, Ta Fadi Hikimar Gwanjon Kadarorin Najeriya a Kasuwa

‘Diyar Atiku ta Zama Lauyarsa, Ta Fadi Hikimar Gwanjon Kadarorin Najeriya a Kasuwa

  • Hauwa Atiku-Uwais ta goyi bayan a bude hannuwa a gayyato mutane domin bunkasa tattalin arziki
  • ‘Diyar Atiku Abubakar ta yarda da manufarsa ta yin gwanjo da wasu daga cikin kadarorin da ke Najeriya
  • Idan Atiku ya karbi shugabancin kasar nan a 2023, Hajiya Atiku-Uwais ta nuna ‘yan kasuwa za su ji dadi

Abuja - Hauwa Atiku-Uwais wanda diya ce ga Alhaji Atiku Abubakar, ta yabi manufar mahaifinta na jawo ‘yan kasuwa wajen kawo cigaban kasa.

A yayin da aka zanta da ita a tashar Channels TV, Hauwa Atiku-Uwais ta ce gwamnatin Atiku Abubakar za ta dage wajen kawo yarjejeniyar PPP.

‘Diyar ‘dan takaran shugaban kasar na jam’iyyar PDP ta ce tsarin hadin-gwiwar gwamnati da ‘yan kasuwa na PPP zai saukaka kasuwanci a Najeriya.

Atiku-Uwais ta ce mahaifinsu yana so ya bar tarihi mai kyau ne shiyasa yake neman shugabanci. Atiku ya neman takararsa ta shida kenan a 2023.

Kara karanta wannan

Saura kwana 5: Kungiyar Arewa ta AFC ta fadi dan takarar da take so ya gaji Buhari

Nasara ta na wajen Atiku a ranar Asabar

A tattaunawar da aka yi da ita Atiku-Uwais ta nuna sa ran Wazirin Adamawa zai lashe zabe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ‘dan takaran na jam’iyyar PDP ya yi nasarar zama shugaban kasa a Mayun 2023, ‘diyarsa ta ce gwamnatinsa za ta yi gwanjon kadarorin kasar.

‘Diyar Atiku
Atiku Abubakar a Abuja Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Saida wadannan kadarori zai jawo a shiga yarjejeniyar PPP, wanda Atiku-Uwais ta ce hakan zai taimaki Najeriya domin zai zaburar da cigaba sosai.

Atiku-Uwais: Amfanin kawo kamfanoni

A kundin manufofinsa ga ‘Yan Najeriya, shi (Atiku) ya yi ta bayani a kan kawo masana’antu da kuma saida kadarorin gwamnati.
Idan ka bada dama ‘yan kasuwa suka shigo, za a samu kamfanoni da ke aiki, kamfanoni za su rika kawo kudi, ana biyan haraji.
Sannan gwamnati za ta samu damar yin harkokin gabanta, a kuma daina dogara kaco-kam da harkar mai.

Kara karanta wannan

2023: Jerin Sunayen Manyan Malaman Addini Da Ke Takara a Zabe Mai Zuwa

A ra’ayina, bude hannuwa da saida kadarori za su yi sanadiyyar da kamfanoni za su shiga yarjejeniya da gwamnati.
Wannan zai bada dama gwamnati ta maida hankali kan aikin gabanta na kawo dokoki da ganin an ji dadin kasuwanci.

- Hauwa Atiku-Uwais

Adadin wakilan zabe a 2023

Kun samu labari INEC ta ce PDP ce ta farko a yawan wakilan zabe sama da 176, 500, Jam’iyyar hamayyar ta na da 11.2% na kason duka wakilan 2023.

Kusan za a iya cewa jam'iyyar NNPP ta bada mamaki domin APC mai mulki ta tsere mata da mutane uku kacal ne a adadin sunayen wakilan zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng