Yanzu Yanzu: PSC Ta Cire Sunan Naja’atu Muhammad Daga Cikin Masu Aikin Zabe
- An cire sunan tsohuwar babbar jigon APC, Hajiya Naja'atu Mohammed, daga cikin masu kula da ayyukan yan sanda yayin zabe
- Hukumar PSC mai kula da ayyukan yan sanda ta maye gurbinta da AIG Bawa Lawal (mai ritaya)
- Ci gaban na zuwa ne bayan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC ya yi watsi da nadin nata
Hukumar Kula da Ayyukan Yan Sanda, PSC, ta janye nadin da ta yi wa Naja'atu Muhammad a matsayin daya daga cikin kwamishinonin da za su kula da harkokin yan sanda yayin babban zabe.
Kakakin hukumar PSC, Ikechukwu Ani, ne ya sanar da ci gaban a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 20 ga watan Fabrairu, jaridar The Cable ta rahoto.
A ranar Lahadi, an ambaci suna Naja'atu cikin jerin kwamishinonin PSC da za su kula da ayyukan yan sanda a yayin zabe mai zuwa.
Sai dai kuma kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC ya yi watsi da nadin, rahoton Punch.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da take bayani, hukumar PSC ta ce bisa al'ada kwamishinoninta ne suke gudanar da ayyukan zabe inda a kan tura su zuwa yankunan da suke wakilta domin sanya idanu a kan harkokin jami'an hukumar.
AIG Bawa Lawal (mai ritaya) zai maye gurbin Naja'atu Muhammad a yankin arewa maso yamma
Har ila yau, hukumar ta maye gurbin Naja'atu da AIG Bawa Lawal (mai ritaya) kasancewar sun fito daga yanki guda.
Wani bangare na sanarwar na cewa:
"An ja hankalin hukumar PSC zuwa ga wata sanarwa da kwamitin PCC na APC ya yi kan nadin Naja'atu da ke wakiltan muradun mata da artewa maso yamma a hukumar a matsayin daya daga cikin wadanda za su kula da ayyukan yan sanda a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu inda ya zarge ta da daukar bangare.
"Sanarwar dauke da sa hannun Daraktan harkokin jama'a kuma kakakin kwamitin yakin neman zaben Tinubu/Shettima, Festus Keyamo, SAN, ya yi watsi da nadin kwamishina Naja'atu a matsayin jagorar shirin."
A karshe hukumar ta jaddada jajircewarta na tabbatar da ganin an yi zabe na gaskiya da amana a 2023 inda yan sanda kan jagoranci harkokin tsaro kamar yadda doka ta tanadar.
A baya mun kawo cewa hukumar PSC ta ambaci sunan Naja'atu Muhammad tare da wasu mutum 44 domin kula da harkokin yan sanda yayin zabe mai zuwa.
Asali: Legit.ng