Zaben 2023: Naja’atu Da Wasu 44 Za Su Sanya Ido Kan Jami’an Yan Sanda

Zaben 2023: Naja’atu Da Wasu 44 Za Su Sanya Ido Kan Jami’an Yan Sanda

  • Tsohuwar babbar jigon APC, Hajiya Naja'atu Mohammed, ta samu babban mukami gabannin babban zaben 2023
  • Hukumar kula da ayyukan yan sanda ta zabi Hajiya Naja'atu da wasu 44 domin jagoranci wajen kula da ayyukan yan sanda yayin gudanar da zabe mai zuwa
  • Kafin ficewarta daga APC, ta kasance darakta a kwamitin yakin neman zaben Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyya mai mulki

Abuja - Hukumar Kula da Ayyukan Yan Sanda, PSC, ta sanar da nada tsohuwar daraktar kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC, Hajiya Naja'atu Mohammed, a matsayin daraktan kula da yan sanda yayi babban zabe.

Hukumar wacce ta nada Naja'atu tare da wasu mutum 44 ta kuma yi barazanar yin maganin duk jami'in da ya nuna rashin da'a a yayin gudanar dfa zabe mai zuwa a fadin jihohi 36 da Abuja.

Kara karanta wannan

CBN: Tinubu Ya Gabatar Da Babban Bukata 1 Bayan An Yi Zanga-Zanga Kan Karancin Naira a Fadin Najeriya

Naja'atu
Zaben 2023: Naja’atu Da Wasu 44 Za Su Sanya Ido Kan Jami’an Yan Sanda Hoto: Punch
Asali: UGC

An fitar da sanarwar ne a ranar Lahadi, 19 ga watan Fabrairu, kwanaki shida kafin babban zaben kasar wanda za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Daily Trust ta rahoto yadda yar siyasar haifaffiyar jihar Kano ta dungi caccakar dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, bayan ta fice daga jam'iyyar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta ce matsalolin da yan Najeriya ke fuskanta yana bukatar ta ci gaba da fafutukar ganin kasar ta inganta ta hanyar tsarkake zuciyarta.

Sai dai kuma, takkadama ya biyo bayan furucin da ta dunga yi kan APC da dan takararta na shugaban kasa.

Hukumar PSC za ta ladabtar da jami'an yan sanda da suka nuna rashin da'a yayin zabe

A wata sanarwa da kakakin hukumar, Ikechukwu Ani, ya saki, ya bayyana cewa mukaddashiyar shugaban hukumar, Clara Ogunbiyi, ce za ta jagoranci shugabannin.

Kara karanta wannan

An samu mafita: Ana tsaka da shan wahalar Naira, Buhari zai yiwa 'yan Najeriya jawabi

Ani ya kara da cewar hukumar ta kuma amince da turan jami'anta fiye da 360 zuwa jihohi 36 na tarayya don sanya ido kan gudanarwar jami'an yan sanda a bakin aikin zabe, rahoton Punch.

Wani bangare na sanarwar na cewa:

"Hukumar za ta hukunta duk jami'in dan sanda da aka samu da rashin da'a kafin, yayin da bayan zabe domin za ta tabbatar da jami'an yan sandan da ke aikin zabe sun tafiyar da aikinsu bisa tsari da doka.
"An samar da lambobin waya da jama'a za su kira don kai rahoton rashin da'ar jami'an yan sanda da ke kan aiki don taimakawa yan Najeriya wajen taka muhimmiyar rawa a zaben.

A wani labari na daban, jam'iyyar APC ta ce dan takararta na shugaban kasa, Bola Tinubu zai ba Atiku Abubakar na PDP mamaki a yankin arewa maso gabas yayin zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel