Muna Tare Da Gwamnoni Kan Lamarin Naira: Shugaban Uwar Jam'iyyar APC

Muna Tare Da Gwamnoni Kan Lamarin Naira: Shugaban Uwar Jam'iyyar APC

  • Bayan awanni ana tattaunawa tsakanin gwamnonin APC da shugabanninta, zama yazo karshe
  • An samu sabani tsakanin wasu gwamnonin jam'iyyar APC da shugaba Muhammadu Buhari kan lamarin Naira
  • Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Adamu, ya bayan zama da gwamnonin yace suna tare da wadannan gwamnoni

Abuja - Shugaban uwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Sanata Abdullahi Adamu, ya sanar da matsayar jam'iyyar game da lamarin sauya fasalin tsabar kudin Naira.

TheCable ta ruwaito Adamu da bayyana hakan bayan zaman sirrin da uwar jam'iyyar tayi da gwamnonin a hedkwatar jam'iyyar dake unguwar Wuse2 Abuja.

Gwamnonin APC dai sun bukaci kotun kolin Najeriya tayi watsi da umurnin shugaba Muhammadu Buhari saboda ya saba doka.

APC govs
Muna Tare Da Gwamnoni Kan Lamarin Naira: Shugaban Uwar Jam'iyyar APC
Asali: Twitter

A bidiyon da hadimin gwamnan jihar Kwara, Yinka Fafoluyi ya fitar a shafinsa na Tuwita, an ji Sanata Abdullahi Adamu yana jawabin goyon baya ga matakin gwamnoni..

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Tinubu Ya Kutsa Wurin Taron Shugaban APC da Gwamnoni Sama da 10, Bayanai Sun Fito

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Abdullahi Adamu ya yi kira da Antoni Janar na tarayya, Abubakar Malami da Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, su bi umurnin kotun koli.

Yace:

"Muna kira ga Antono Janar na tarayya da gwamnan bankin Najeriya su girmama umurnin kotun koli da tayi har ila yau."
"Wannan zama na kira ga shugaban kasa ya sa baki wajen magance wadannan matsaloli dake haddasa wahala cikin al'umma da tattalin arziki."

Buhari vs Gwamnoni: An shiga tattaunawan sirri tsakanin Gwamnoni da Shugabannin APC

Gwamnonin jam'iyyar APC sun shiga takun saka da shugaban kasa kuma jagoran jam'iyyar a kwanakin bayan game da lamarin sauya fasalin Naira.

Akalla gwamnoni goma sun shigar da shugaba Muhammadu Buhari kotun koli kuma kotun ta fara biya musu bukata.

Kotun koli tayi umurinn cewa a cigaba da amfani da tsaffin kudin har zuwa lokacin da zata yanke hukunci kan lamarin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban APC Ya Shiga Ganawar Sirri Da Gwamnonin APC Kan Rikicin Naira

Ana tsaka sai shugaban kasan ya bada umurnin a dawo da tsaffin N200 kadai amma a cigaba da amfani da sabbi kuma kowa ya mayar da tsaffin N500 da N1000 bankin CBN.

Wannan abu ya fusata gwamnoni inda wasu suka fara sukansa kamar yadda ba'a taba gani ba.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, da daren Alhamis ya gabatar da jawabi irin na Buhari kuma yace al'ummar jiharsa su cigaba da amfani da tsaffin kudinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel