Shugaban APC Ya Shiga Ganawar Sirri Da Gwamnonin APC Kan Rikicin Naira

Shugaban APC Ya Shiga Ganawar Sirri Da Gwamnonin APC Kan Rikicin Naira

  • Rana bata karya sai da uwar 'da taji kunya, an shiga zaman uwar jam'iyya da gwamnonin APC
  • An samu sabani tsakanin wasu gwamnonin jam'iyyar APC da shugaba Muhammadu Buhari kan lamarin Naira
  • Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Adamu, ya kira zama da gwamnonin don ganin yadda za'a yi

Abuja - Shugaban uwar jam'iyyar All Progressives Congress APC, Sanata Abdullahi Adamu, ya shiga ganawar sirri da daukacin gwamnonin jam'iyyar yanzu haka.

Gwamnonin dake hallare sun hada da Nasir El-Rufa'i na jihar Kaduna, Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa, Gwamna Simon Lalong na Plateau, da gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja.

Hakazalika akwai Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe da kuma Gwamna Muhammad Inuwa na jihar Gombe.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Muna Tare Da Gwamnoni Kan Lamarin Naira: Shugaban Uwar Jam'iyyar APC

Apc govs
Shugaban APC Ya Shiga Ganawar Sirri Da Gwamnonin APC Kan Rikicin Naira Hoto: @APCNigeria
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel